✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwamitin amintattu ya fara sasanta tsakanin Gwamna da Olubadan

Kwamitin amintattun mutane a masarautar Ibadan ya fara daukar matakin sasanta takaddama tsakanin Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo da Olubadan na Ibadan Oba Saliu…

Kwamitin amintattun mutane a masarautar Ibadan ya fara daukar matakin sasanta takaddama tsakanin Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo da Olubadan na Ibadan Oba Saliu Adetunji a kan batun daukaka darajar wasu hakimai zuwa matsayin sarakuna da gwamnan ya yi a kwanakin baya, matakin da shi kuma Olubadan ya ki amincewa da shi.

Matakin farko da kwamitin ya dauka shi ne, ganawar sirri da ya yi da Gwamna Ajimobi, a inda suka tattauna a kan yadda kowane bangare zai janye karar da ya shigar a kotu domin shawo kan matsalar a cikin gida.

Shugaban kungiyar ’yan asalin Ibadan, Cif Yemi Soladoye ne ya jagoranci wasu wakilan kungiyar da hadin gwiwar kwamitin amintattun mutane da wasu dattawa da masu ruwa da tsaki da suka yi wannan ganawa da gwamna a ofishinsa a Ibadan.

Da yake yi wa ’yan jarida bayani jim kadan bayan ganawar, Cif Yemi ya ce, a karshen watan nan na Janairu ne kwamitin amintattun zai yi wa duniya cikakken bayani da irin shawarwarin da za su kai ga nasarar shawo kan wannan al’amari da ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin gwamnan da Olubadan.

Wata biyar da suka gabata ke nan da aka fara sa-in-sa a kan wannan al’amari, a lokacin da Gwamna Ajimobi ya tabbatar da daukaka matsayin wasu hakimai zuwa sarakuna, wanda Olubadan ya ce ba zai amince da aukuwar haka a masarautar Ibadan ba.  Wasu fitattun ’yan siyasa ’yan asalin Ibadan sun yi ta zargin juna da ruruta wutar fitinar.

Tun daga wancan lokaci ne dangantaka ta sukurkuce gaba daya a tsakaninsu, inda Olubadan y ace a zamanin mulkinsa ba zai taba amincewa da daukaka darajar hakimai zuwa sarakuna a baki ba tare da masarauta ba. Hakan ne ya haifar da ci gaba da kazancewar al’amarin, inda hart a kai ga aka taba yin harbe-harben bindiga a fadar Olubadan a daidai lokacin da yake nada sababbin hakiman da za su maye gurbin wadanda Gwamna ya daukaka darajarsu zuwa sarakuna. Haka kuma, yunkurin tube Olubadan daga karaga da wadannan sababbin sarakuna 21 suka yi ya kara ruruta wutar fitinar.

Ci gaba da kazantar al’amurin ne ya sa masu ruwa da tsaki suka kafa kwamitin amintattun mutane da suka fara duba yiwuwar shawo kan wannan matsala a cikin gida ba tare da an je kotu ba.