✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kwamishinonin Ganduje 7 sun ajiye mukamansu saboda takara a 2023

Ganduje ya nemi duk masu rike da mukaman siyasa da su yi wa Dokar Zabe biyayya.

Kawo yanzu Kwamishinoni bakwai ne a Jihar Kano suka ajiye mukamansu a ranar Lahadi, tare da wasu daga cikin hadiman gwamnati da zimmar tsayawa takara a babban zaben 2023 da ke tafe.

Duk wannan dai na dauke cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Ganduje kan kafafen sada zumunta Abubakar Aminu Ibrahim ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Daga cikin wadanda suka ajiye mukamansu a Jihar Kano, akwai Kwamishinan Ilimi, Alhaji Sanusi Sa’idu Kiru da ya sauka daga mukaminsa don takarar dan Majalisar Tarayya a Kiru da Bebeji.

Honarabul Musa Iliyasu Kwankwaso, Kwamishinan Raya Karkara ya bayyana ajiye mukaminsa domin shiga takarar dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kura da Madobi da Garun Malam.

Kwamishinan Ayyuka na musamman, Alhaji Muntari Ishaq Yakasai ya sauka daga mukaminsa don takarar dan Majalisar Tarayya a Karamar Hukumar Birni.

Haka kuma, Kwamishinan Kasafin Kudi na Jihar Kano, Alhaji Nura Muhammad Dankadai ya ajiye mukaminsa don takarar dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Tudun Wada da Doguwa.

Shi ma Kwamishinan Kananan Hukumomi na Kano Alhaji Murtala Sule Garo ya sauka daga mukaminsa don takarar Gwamnan Kano a zaben na badi.

Kazalika, Kwamishinan Ma’aikatar Al’adu da Yawon Bude Idanu na Kano Ibrahim Ahmad Karaye ya sauka daga mukaminsa don takarar dan majalisar tarayya mai wakiltar Karaye da Rogo.

Na baya bayan nan da hadimin gwamnan ya bayyana shi ne, Hon. Mahmoud Muhammad Santsi, Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano da ya sauka daga mukaminsa domin shiga takarar dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Gabasawa da Gezawa.

Kamar yadda Gidan Rediyon Freedom ya ruwaito, Babban Daraktan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano Dokta Aliyu Musa Aliyu ya ajiye mukaminsa domin takarar dan majalisar tarayya na Kananan Hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure.

Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya bai wa masu rike da mukaman siyasa da ke sha’awar takara umarnin ajiye aiki domin biyayya ga Dokar Zabe.