Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kaduna, Mudassir Abdullahi ya umurci daukacin shugabannin ofis-ofis din ’yan sanda da su kamo akalla dillalin kwayoyi daya nan da kwanaki bakwai.
Ya bayar da umurnin ne a lokacin da yake jawabi ga shugabannin kungiyoyi da jami’an ’yan sanda a Babban Ofishin ’yan sanda shiyyar Zariya a yayin ci gaba da rangadin da yake yi don sanin halin da jami’ansa suke ciki.
Kwamishinan ya ce kashi 70 cikin dari na masu aikata fyade da sauran miyagun laifuka musamman a Arewa masu ta’ammali da miyagun kwayoyi ne, lamarin da ya ce dole a tashi tsaye domin daukar matakan da suka dace.
Ya ce duk wanda aka kama da aikata fyade ba za su saurara ba wajen daukan matakin da ya dace.
A game da wata mata da ake zarginta da bata kananan yara ’yan shekara 6 da haihuwa ta hanyar kwakule, kwamishinan ’yan Sandan ya ce da zarar sun kammala bincike za su gabatar da ita gaban Kotu.