✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kwamishinan Lafiyar Jihar Binuwai ya rasu

Fadar Gwamnatin jihar Benuwe ta ce mutuwarsa ta jefa ta cikin dimuwa.

Kwamishinan Lafiya na Jihar Binuwai da ke Arewacin Najeriya, Dokta Emmanuel Ikwulono, ya riga mu gidan gaskiya.

Sanarwar da fadar gwamnatin jihar ta fitar ta ce Kwamishinan ya mutu ne bayan an yi masa tiyata a wani asibiti da ke birnin Jos kan wata cuta da ba a bayyana ba a ranar Laraba.

“Kwamishinan ya halarci zaman Majalisar Zartarwa na gwamnatin jihar da aka gudanar a makon jiya kuma daga bisani aka yi masa tiyatar.

“Mutuwarsa a Yammacin yau (Laraba) ta dimauta mu”, inji sanarwar.

A ranar 5 ga watan Agustan 2020 ne aka rantsar da marigayi Ikwulono a matsayin Kwamishinan Lafiya da yi wa Al’umma Hidima, mako guda bayan da Dokta Sunday Ongbabo ya sauka daga mukamin.