Kwamishinan Harkoki na Musamman a Jihar Akwa Ibom, Mista Ini Ememobong, ya yi murabus daga muƙaminsa biyo bayan sauya sheƙar Gwamna Umo Eno daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.
- Sallah: Gwamna Inuwa ya yi kiran sadaukarwa da haɗin kai
- Tinubu ba zai canza Kashim a matsayin mataimakinsa ba a 2027 – APC
Gwamna Eno ya faɗa wa kwamishinoninsa cewa duk wanda ba ya son bin sa zuwa APC ya ajiye aikinsa.
Ememobong, ya ce yana girmama ra’ayin gwamnan, amma ba zai iya binsa APC ba.
“Ba zan iya yin wannan tafiya ba,” in ji Ememobong.
“Na yarda da siyasar aƙida. Na gode wa gwamna bisa ƙauna da ya nuna min, amma dole na tsaya kan abin da nake da yaƙini a kai.”
A ranar Juma’a ne, Gwamna Eno, ya sanar da ficewarsa daga PDP zuwa APC, inda ya ce ya yanke hukuncin ne bayan dogon nazari.
“Na tuntuɓi mutane daga ko ina a cikin jihar,” in ji Eno.
“Wannan shawara ce da ta dace da lokacin da muke ciki. Mun shiga APC ba don mu samu rauni ba, sai don mu ƙara ƙarfi.”
Da wannan sauyin, APC na da iko a jihohi huɗu cikin shida da ke yankin Kudu Maso Gabas, sai Jihohin Ribas da Bayelsa kawai suka rage a hannun PDP.