✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ba zai canza Kashim a matsayin mataimakinsa ba a 2027 – APC

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta musanta labarin da ake ta yadawa cewa akwai yiwuwar Shugaban Kasa Bola Tinubu ya canza mataimakinsa, Kashim Shettima…

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta musanta labarin da ake ta yadawa cewa akwai yiwuwar Shugaban Kasa Bola Tinubu ya canza mataimakinsa, Kashim Shettima gabanin zaben 2027.

APC ta bakin mataimakin shugabanta na kasa na shiyya Kudu maso Gabas, Dr Ijeoma Arodiogbu, ta musanta zargin inda ta ce wasu ne suka kirkire shi domin su kawar da hankalin mutane.

Ijeoma ya ce, “Yanzu na fara jin labarin. Akwai kyakkyawar alaka da fahimtar juna tsakanin shugaba Tinubu da mataimakinsa Kashim.

“Kashim babban jigo ne a wannan tafiya. Mutum ne mai kwakwalwa sosai, yana da alkibla kuma da shi ake yin komai a cikin wannan gwamnatin. Wannan jita-jitar kawai maganar siyasa ce da aka kirkire ta domin a raba kan mutane.,” in ji shi.

Mataimakin shugaban ya kuma ce ba abin mamaki ba ne don an ji irin wadannan maganganun a daidai lokacin da ake tunkarar kakar zabe ta 2027,.

Sai dai ya ce shugaban kasa da mataimakin nasa suna tare sannan suna da sahalewar jam’iyyarsu.

Jita-jitar dai ta fara ne jim kadan bayan gwamnonin APC 22 da shugabannin Majalisar Dokoki ta Kasa da ma sauran shugabannin jam’iyyar sun amince da Tinubu a matsayin dan takara daya tilo na jam’iyyar a zabe mai zuwa.

Gwamnan jihar Imo kuma shugaban Kungiyar Gwamnonin APC, Hope Uzodinma ne dai ya fara gabatar da bukatar, sannan gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya goyi bayansa a yayin taron kasa na APC da aka gudanar a dakin taro na fadar shugaban kasa da ke Abuja a kwanakin baya.