Kwamishinan Kasashen Waje, Zane-Zanen Gargajiya, Al’adu da Yawon Bude Ido na Jihar Anambra, Christian Madubuko ya yi murabus daga mukaminsa.
Mista Madubuko a cikin wasikarsa ta yin murabus, ya yi zargin cewa cin hanci da rashawa sun yi kaka-gida a tsarin gwamnatin jihar, inda ya nemi Gwamna Willie Obiano da ya farka ya kuma tsayayye a kan sha’anin gwamnatinsa.
- Sergio Ramos da Messi za su koma PSG, Chelsea za ta raba gari da Lampard
- Ganduje: Shirin Shekarau da Kwankwaso na ta da kura kan 2023
- Mutum 1,204 sun kamu da cutar Coronavirus a Najeriya – NCDC
- An sake kara kudin wutar lantarki da kashi 50%
Wasikar ta ce, “Ina matukar farin ciki da nuna godiya a tsawon lokacin da muka shafe muna yi wa jiharmu hidima kuma tabbas shekaru ukun da muka yi tare suna cike da darussa masu kyau da kuma sabanin haka.
“A gwagwarmayar da muka yi ta yakar masu cin hanci da rashawa da suke yi wa tattalin arzikin jihar ta’annati, sau tari an gabatarwa wa gwamnan korafe-korafe a kaina ana zargi na da aikata wasu munanan abubuwa da za su dagula al’amura ko kawo hargitsi a jam’iyyarmu ta APGA, inda aka rika shawartar sa ya kore ni kafin in yi wa jam’iyyar mummunar illa.
“A lokuta da dama, jakadun zalunci sun yi kokarin ba ni cin hanci na miliyoyin Naira, amma na sa aka kamu su wanda har gwamnan ya rika yaba wa da hakan a zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar.
“Dalilin haka ya sanya gwamnan ya ba ni jagoranci wasu muhimman ma’aikatu uku a matsayin Kwamishina.”
“Duba da ire-iren wadannan ababe da suka rika faruwa, ta bayyana karara cewa a yayin da kake yaka da cin hanci da rashawa, ita ma rashawar tana mayar da martani ta fuskoki da dama.
“Yanzu na fahimci cewa, wannan shi ne babban dalilin da ya sanya Najeriya ba za ta taba ci gaba kamar Turai ba; kokarin taimakawa jiharmu ya sa na dawo daga Kasar Australiya domin ganin jihar ta bunkasa.
“Gaskiya na yi aiki tukuru domin ganin wannan buri nawa ya tabbata, wanda hakan ya sanya muka kirkiri kotukan tafi-da-gidanka muka rika daure barayin gwamnati tare da habaka samun kudin shiga a jihar.
“Na yi kasadar sadaukar da raina domin kawo ci gaba a Jihar ta hanyar yakar wadannan miyagu masu manufofi na son zuciya kuma na daure da dama, amma a yanzu rayuwata tana cikin hatsari.
“Sau uku ana turo ’yan bindiga su kawo min hari, haka kuma jami’an da ke satar kudaden shiga na Jihar sun kai min hari a lokuta daban-daban a Babbar Kasuwar Onitsha.
“Duk wannan yunkuri na faruwa ne saboda a hana ni fallasa masu tatsa da karkatar da dukiyar gwamnatin Jihar zuwa aljihunsu suna jefa sauran al’umma cikin mawuyancin hali.
“Da wannan nake ba Mai Girma Gwamna shawara, da ya tashi tsaye ya fuskanci al’amuran jagoranci kuma ya rataya duk wani nauyi na gwamnati a wuyansa.
“Dalili kuwa shi ne, a karshe duk yadda ta kasance shi za a zarga idan aka samu cikas a sha’anin jagoranci kuma shi za a yaba wa idan ta gyaru domin kuwa dukkanin wani alhaki zai koma gare shi ne.
“A takaice, ina ganin na yi wa kowa adalci kuma na yanke shawarar ajiye aiki na kama gabana,” inji Dokta Maduboko.
A tsawon shekaru uku da aka shafe ana damawa da Dokta Maduboku a gwamnatin Jihar Anambra, ya rike mukamin Kwamishina a Ma’aikatar Masana’antu da Kasuwanci, Sufuri da kuma Harkokin Kasashen Waje, Zane-Zanen Gargajiya, Al’adu da Yawon Bude Ido.