Kwamishinan Kimiyya da Kirkira na Jihar Gombe, Abishai Andirya ya yi murabus daga mukaminsa kwana tara kafin zaben gwamna.
Mista Andirya ya ajiye mukaminsa ne a ranar Laraba, wata uku bayan Gwamna Inuwa Yahaya ya nada shi a matsayin kwaminishina a jihar.
- Buhari ya je Maiduguri jajanta wa ’yan Kasuwar Monday
- Na tabbata Tinubu zai kai Najeriya tudun-mun-tsira —Aisha Buhari
Ya bayyana manema labarai cewa dalilinsa na ajiye aiki shi ne, shi Kwamishina ne kawai a baki, domin kuwa, tun da gwamnan ya nada shi a mukamin, ba ya iya ganin gwamnan sai a wajen zaman Majalisar Zartarwa.
Ya ce,“Ni dan jam’iyyar APC ne tun a shekarar 2015, mun yi wa APC aiki har ta ci zabe a 2019, tun a baya gwamna ya yi alkawari ba ni mukamin kwamishina, amma bai ba ni ba sai bayan da ya sauke wasu kwamishinoninsa a watan Oktoba,” in ji shi.
Mista Andirya ya yi korafin cewa duk da cewa ya zama kwamishina, amma ba ya iya taimakawa al’ummarsa, saboda ba ya iya ganin gwamna, shi dai yana sunan Kwamishina ne kawai, amma babu wani abu da yake samu da zai iya yi wa al’ummarsa.
Ya ce ya yi iya kokarinsa don ya samu ganin gwamnan ya bayyana masa matsalolinsa ya gagara, sai da takwaorrinsa kwamishinoni suka bayyana masa cewa idan yana son ganin gwamnan sai dai kawai a lokacin zaman Majalisar zartarwa.
A takardar ajiye aikin da wakilinmu ya samu ta nuna cewa mista Abishai Andirya ya ajiye aikin ne tun a ranar 20 ga watan Fabarairu.
Andirya, ya gode wa Gwamna Inuwa Yahaya da ya ba shi dama ya zama Kwamishina a gwamnatinsa daga ranar 1 ga watan Nuwamba 2022 zuwa 20 ga watan Fabarairu 2023.