Kwamandojin Boko Haram da suka mika wuya ga sojojin Najeriya suna neman ’yan kasar su yafe musu kan irin ta’asar da suka tafka.
Daga cikin Kwamandojin Boko Haram da suka mika wuya a Jihar Borno, har da babban mai hada wa kungiyar ababan fashewa, wanda ake wa lakabi da Mala Musa Abuja da mataimakinsa mai lakabin Abu Darda.
A lokacin gabatar da kwamandojojin Boko Haram din da mayakan ga ’yan jarida, sun yi ta daga kwalaye masu dauke da rubutun neman yafi da zama lafiya; Daga cikinsu akwai wanda aka rubuta, “’Yan Najeriya mun tuba, ku yafe mana.”
Kakakin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Manjo-Janar, Onyema Nwachukwu, ya ce mayaka da kwamnadojin Boko Haram din tare da ma iyalansu sun mika wuya ne bayan dakarun rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) sun matsa musu da hare-hare a yankin Arewa maso Gabas.
SAURARI: Za a sauki tsauraran matakai a kan direbonin manyan motoci:
Janar Nwachukwu ya ce kwamandoji da mayakan Boko Haram 335 ne suka mika wuya tare da iyalansu mutum 746 da suka hada da kananan yara da mata, ciki har da daya daga cikin daliban Chibok.
“Mun gano cewa yawan mika wuyan da mayakan da iyalan nasu suka yi ya biyo bayan matsin da sojoji suka yi da hare-hare a kan maboyansu da ke cikin dazuka.
“Suna kuma fama da yunwa da rashin lafiya da rikicin cikin gida da ya addabin kungiyar, sai kuma rashin gamsuwa da abubuwa da ke gudana a cikin tafiyar kungiyar da suransu.”
Shi ma “Babban mai hada wa kungiyar bom wanda aka fi sani da Mala Musa Abuja da mataimakinsa Abu Darda tare da iyalansu da mabiyansu sun mika wuya ga dakarun Operation Hadin Kai (OPHK) a Karamar Hukumar Bama ta Jihar Borno,” inji shi.
“A lokacin GOC ya yaba musu da tubar da suka yi, sayyana ya bukace su da su jawo hankalin abokansu da ke cikin daji su fito su ajiye makamansu domin su zauna lafiya.
“Janar Eyitayo ya ce za a ba wa tubabbun horo domin sauya tunaninsu kafin daga baya a bar su su koma cikin al’umma da zama.”
“Rundunar Sojin Najeriya ta yanke shawarar za ta yi amfani da dabarun da ba na soji ba ta hanyar tattaunawa da Mala Abuja da Abu Darda da sauran mayakan da suka tuba domin kaiwa ga nasara a yakin da take yi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.”