✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwamandojin Boko Haram 4 Sun Mika Wuya Ga Sojoji

Wasu manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram hudu sun mika wuya ga sojojin Najeriya a Jihar Borno.

Wasu manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram hudu sun mika wuya ga sojojin Najeriya a Jihar Borno.

Wata majiya mai tushe ta ce kwamandojin sun mika makamansu ne a ranar 12 ga wannan wata na Disamba, 2022 ga sojojin Operation Hadin Kai (OPHK) da ke sintiri a Karamar Hukumar Gwoza ta jihar.

Majiyar tsaron ta ce wadanda suka mika wuyan tsoffin kwamandojin Abubakar Shekau ne a Sansanin Njimiya da suka koma Kungiyar ISWAP bayan harin da ISWAP ta kai Dajin Sambisa a watan Mayun 2021, wanda ya yi sanadin mutuwar Shekau.

Sai dai daga baya su hudun sun yi tir da ISWAP, inda suka gudu zuwa Dajin Sambisa suka kafa tanti suka ci gaba da aikata ta’asarsu a matsayin ’yan Boko Haram.

Majiyar tsaron ta ce ’yan ta’addan sun fito ne daga Dajin Sambisa kuma sun mika wuya ne saboda tsoron hare-haren sojojin Najeriya ta sama da kasa kan maboyar ’yan ta’adda a bangare guda, da kuma hare-haren ISWAP a daya bangaren.

Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), Manjo-Janar Christopher Musa, ya ce kawo yanzu ’yan Boko Haram kusan 83,000 ne suka mika wuya kuma ana ci gaba da gyara halayensu a wurare daban-daban.

Musa ya ce kwamandojin sun mika wuya ne saboda kofar ragon da a kullum sojojin Najeriya ke musu a maboyarsu da ke kungurmin Dajin Sambisa da wasu sassan da ke fili.