✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kwamandan Hisbah ya yi bankwana da ma’aikatan hukumar

Ni dai na yafe wa duk wanda ya saba min a iya zaman da muka yi da ku.

Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Shaikh Harun Muhammad Ibn Sina, ya nemi afuwar abokan aikinsa a daidai lokacin da yake yi musu bankwana na barin aiki.

“Ina neman afuwar wadanda na batawa a yanayi na aiki bisa kuskure. Ina neman ko yafe min.

“Ni dai na yafe wa duk wanda ya saba min a iya zaman da muka yi da ku.

“Wannan shi ne kusan lokaci na karshe na zamana a wannan hukuma.”

Ustaz Ibn Sina ya yi kira ga abokan aikinsa da su ci gaba da tsaya wa tsayin daka wajen gudanar da ayyukansu bisa gaskiya da rikon amana.

Da yake yi wa Aminiya karin haske, Shugaban na Hisbah ya bayyaba cewa bisa ka’idar aiki ya kammala wa’adin aikinsa na shekaru hudu, dalili ke nan da ya fara tattara kayansa don barin ofishinsa.

Aminiya ta ruwaito Ibn Sina yana kira da ma’aikatan hukumar da su dage addu’a don samun mutum nagari da zai maye gurbinsa a matsayin shugaban hukumar

“Ina so ku yi addu’a Allah Ya ba ku shugaban da ya fi ni wanda kuma zai zama mai tausayinku da son ci gabanku tare kuma da zama shugaban da zai ci gaba da gudanar da ayyukan alheri a wannan hukuma mai albarka.”

Sai dai har zuwa yanzu babu wata takardar barin aiki da Shugaban Hukumar ya sanya wa hannu a hukumance.