✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwallon tenis ba na masu kudi ne kawai ba – Kabiru

Wani fitaccen dan kwallon tenis mai suna Kabiru Ibrahim, ya ce kwallon tenis ba na masu kudi ba ne kawai. Ibrahim wanda Bafulatani ne da…

Wani fitaccen dan kwallon tenis mai suna Kabiru Ibrahim, ya ce kwallon tenis ba na masu kudi ba ne kawai.

Ibrahim wanda Bafulatani ne da ke bugawa kungiyar kwallon kafa mai suna Team Fulani  da ke Abuja, ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa ta musamman da Aminiya, a Abuja, a karshen makon da ya gabata.

Ya bayyana cewa mafi yawan ’yan wasan kwallon Tenis da suka yi fice a duniya ’ya’yan talakawa ne.

“Idan ka duba za ka ga cewa yawancin ’yan wasan kwallon tenis da suka yi fice a duniya ba ’ya’yan masu kudi ba ne. Saboda haka kwallon tenis wasa ne da kowa zai iya yi”. Inji shi.

Matashin dan wasan, dan kimanin shekaru 18 a duniya da ke zaune a unguwar Ruga da ke Abuja ya bayyana cewa wasan tenis wasa ne da mutum zai iya dogara da shi a rayuwarsa.

Ya ce abin da dan wasa yake bukata shi ne ya mayar da hankali kuma ya samu wanda zai dauki nauyinsa.

Ya bayyana cewa idan dan wasa ya mayar da hankali babu shakka zai cimma burin da ya sanya a gaba.

Ya kara da cewa mai horar da ’yan wasan Tenis mai suna Koci Tobi ne ya yi sanadin shigarsa cikin wasan kwallon tenis.

Ya ci gaba da cewa burinsa shi ne ya yi fice a duniya kamar yadda  sauran ’yan wasan tenis suka yi fice.

Ya shawarci matasa su tashi tsaye su shiga wasan motsa jiki don cimma burin da suka sanya a gaba.