✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya cinna wa mutane wuta suna sallar Asuba a masallaci a Kano

Ana tsaka da Sallar Asuba a safiyar Laraba a masallacin ne mutumin ya zuba musu fetur ya kyasta wuta sannan ya kulle su a ciki.

Wani matashi ya banka wa masallaci wuta a yayin da ake tsaka da Sallar Asuba a Jihar Kano.

Shaidu sun ce ana tsaka da Sallar Asuba a safiyar Laraba a masallacin ne mutumin ya shigo ya rurrufe kofofin ya zuba makamashi ya kyasta wuta sannan ya kulle su a ciki ya tsere.

“Da kyar mutanen da suke waje suka yi nasarar balle kofar su ceto na cikin masallacin,” in ji wani mazaunin yankin.

Wani dattijo da ke salla a masallacin ya ce sai da aka yi raka’a daya an ffara raka’a ta biyu wanda ake zargin ya sa wutar.

Malamin wanda ya ce ba da shi aka fara sallar ba saboda ya makara, ya bayyana yadda mutane suka kokkone a masallacin, kuma akasarin wadanda suka konen dattawan garin ne.

Aminiya ta samu bayani cewa akalla mutane 28 ne suka samu mummunan kuna a sakamakon wutar da mutumin ya cimma a masallacin fa ke garin Larabar Abasawa da ka Karamar Hukumar Gazawa ta jihar.

Wakilinmu ya ruwaito cewa an kai mutanen da suka kone asibiti domin ba su kulawa a Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke birnin Kano.

Majiyoyi a yankin sun ce kimanin mutane 40 ne suke sallar a masallacin a lokacin da mutumin ya yi wannan aika-aika.