✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwalliyar ’mai da tsohuwa yarinyaa’

Mace duk tsufanta ba ta son a ce da ita ta tsufa. Kullum tana so a rika ganinta kamar yarinya ko ’yan mata. Koda gidan…

Mace duk tsufanta ba ta son a ce da ita ta tsufa. Kullum tana so a rika ganinta kamar yarinya ko ’yan mata. Koda gidan biki za ta sai a ga tana kokarin ta ga ta fi matasan wajen ado da takalmi ko riga da kuma kwalliya.Don haka ne a yau muka kawo muku yadda za a magance irin wadannan matsalolin.

Kwalliyar ido:
Babban kuskuren da mata suke yi idan sun zo yin kwalliya a idanunsu shi ne, maimakon su sanya kwalli ko gazal a idon kawai, sai su hada bakin kwallin a fatar saman idanu. Idan mace ta dan manyanta bai kamata tana irin wannan kwalliyar ba. Sai dai ta zabi daya. Ko ta sanya gazal a ido ta bar saman idon ko kuma ta shafa eye shadow a fatar ido ta bar idon ba kwalli. Yin duka biyun suna sanya ta ta yi kama da dodo.
Gyaran fatar fuska da jiki:
Idan shekaru sun ja, lallai ne a kula da fatar jiki fiye da kwalliyar da za a yi a fuska. Sirrin yin hakan shi ne, ana son fatar mace ta zama kamar ba ta yi kwalliya ba. Don haka, ya kamata a shafa hodar fandesho dai-dai da kalar fatar fuska don boye tattarewar fuska da kuma tsufa. Idan akwai kuraje a fatar jiki ko fuska, za a iya amfani da man concealer a hada da hodar fandesho don boye wadannan tabo ko kurarrajin fata. Kada a manta amfani da kalar da ta dace da fata wajen sanya hodar fandesho.
Baki:
Ba lallai ba ne a nemi kala mai haske sosai wajen sanya jan baki. Koda ja ne za a iya sanya jan da bai cika haske ba. Ko kuma man baki kadai ya wadatar. Idan aka gwada wadannan kwalliyar lallai za a ga tsohuwa ta zamo yarinya.