Wasu jami’an ’yan sanda uku da ba a kai ga tantance su ba sun kife a hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Ijaw ta Kudu dake jihar Bayelsa.
Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya faru ne ranar Asabar, ana jajiberin zaben cike gurbi da yake gudana a mazabun dan Majalisar Dattawa biyu na jihar.
- Mutum 18 sun mutu a nutsewar kwalekwale a Bauchi
- Jami’ar Amurka ta musanta nada Ganduje a matsayin farfesa
’Yan sandan dai sun gamu da ajalinsu ne lokacin da suke kan hanyar su domin zuwa wurin da za su kula da da zabe a yankin mai yawan rafuka lokacin da suka hadu da iftila’in kifewar kwale-kwalen.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Mista Mike Okoli ya shaida wa ‘yan jarida cewa kimanin jami’ansu 5,000 aka tanada domin kula da zaben a mazabun Majalisar Dattawa na Bayelsa ta Yamma da ta Tsakiya.
A nasa bangaren, kakakin Rundunar ’Yan Sanda na jihar, SP Asinim Butswat ya tabbatar da faruwar lamarin, ko da dai ya ce ya zuwa yanzu ba su kai ga tabbatar da hakikanin yawan wadanda ya shafa ba.
Sai dai ya yi alkawarin yin karin bayani da zarar sun kammala bincike a kai.