Cutar kwalara ta kashe mutum bakwai tare da kwantar da wasu shida a asibiti a garin Garko a Karamar Jukumar Akko, Jihar Gombe.
Wannan na dauke ne cikin wani jawabi da Kwamishinan Lafiyan Jihar, Dokta Habu Dahiru ya sanya wa hannu a ranar Alhamis, yana mai tabbatar da barkewar cutar.
- Buhari ya nada sabon Babban Hafsan Sojin Kasa
- Da dumi-dumi: Allegri zai sake komawa Juventus
- EFCC ta kwace gidajen ma’aikacin Fadar Shugaban Kasa
“A duk farkon yanayin damina ana samun barkewar kwalara saboda zuwan gurbataccen ruwa da mutane ke sha,” a cewarsa.
Kwamishinan ya ce rahoton farko da aka samu na barkewar cutar a kauyen Kalajanga ne, inda wani yaro mai shekara biyu a duniya ya rasu.
Ya ce cikin mako guda mutum 32 sun kamu da cutar amma an yi saurin ba su agaji sun kuma warke baki dayansu.
Kazalika, bincikensu ya gano cewa yawancin mutane na kamuwa da cutar ta kwalara ce saboda shan gurbataccen ruwa.
Dokta Dahiru, ya ce sun kafa kwamiti na musamman da zai bibiyi cutar da kuma matakan da za su bi don dakile yaduwarta a tsakanin jama’ar jihar.
Kwamishinan ya ja hankalin jama’a kan muhimmancin amfani da tsaftaccen ruwa da kuma tsaftar muhalli.