✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwalara ta kashe mutum 10 a Afrika Ta Kudu

Hukumomin kiwon lafiya a kasar sun gargadi mutane da cin gurbataccen abinci da ruwa.

Cutar amai da gudawa ta kashe akalla mutum 10 a kusa da Pretoria babban birnin kasar Afirka ta Kudu, in ji hukumomin kiwon lafiya a kasar.

Ma’aikatar lafiya a lardin Gauteng ta Pretoria ta ce mutum 95 sun ziyarci wani asibiti wa da aka gano alamun kwalara da suka hada da gudawa, ciwon ciki da tashin zuciya.

Gwajin da aka yi a ranar Lahadi ya tabbatar da cewa akalla mutum 19 ne suka kamu da cutar kwalara, in ji ma’aikatar, cikin wata sanarwa, inda ta kara da cewa mutum 37 na jinya a asibitin.

Wadanda abin ya shafa sun hada da yaro dan shekara uku da manya tara.

Nomantu Nkomo-Ralehoko, shugaban kula da lafiya na lardin, ya ce ana kara daukar karin ma’aikata da suka hada da likitoci da ma’aikatan jinya, domin shawo kan barkewar cutar.

“Muna so mu sake jaddadawa tare da kira ga jama’a da su guje wa cin gurbataccen abinci ko gurbataccen ruwa sannan su rika wanke hannu da sabulu,” in ji Nkomo-Ralehoko.

Ana kamuwa da cutar kwalara ne ta hanyar gurbataccen abinci ko ruwa.

Tun da farko, hukumomin birnin Pretoria sun bukaci mazauna Hammanskraal da kewaye da kada su sha ruwan famfo, bayan bullar cutar.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta dora alhakin karuwar bullar cutar a duniya kan talauci, rikici da sauyin yanayi.