Akalla mutum biyu sun rasu bayan barkewar cutar Kawalara a wajen da aka killace tubabbun ’yan Boko Haram da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Kwamishiniyar Mata da Walwalar Jama’a ta jihar, Hajiya Zuwaira Gambo ce ta tabbatar da hakan ga manema labarai a Maiduguri.
Sai dai ta karyata labaran da ake yadawa kan mutuwar mutane da dama, inda ta ce mutum biyu kawai suka tabbatar da rasuwarsu kawo yanzu.
Ta ce, “Ban san daga inda aka samo wadannan alkaluman ba, amma ina mai tabbatar muku cewa mutum biyu ne kawai suka mutu.”
Ta ce tuni jami’ai daga Ma’aikatar Lafiya ta jihar suka isa wajen don yin feshin magani da kuma kwashe wadanda aka yi wa maganin cutar domin a killace su da takaita yaduwar cutar.
Cutar Kwalara ko Amai da Gudawa dai cuta ce da kwayar cutar ‘bacteria’ ke haddasawa, kuma za ta iya kisa cikin ’yan sa’o’i da kamuwa da ita.
Mutane kan kamu da ita ne idan suka ci abinci ko abin sha da yake dauke da kwayar cutar.