✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Kwadayi da son kai sun rufe idanun ’yan siyasa a Najeriya’

’Yan siyasa na mallake mutanenmu saboda duhu na jahilci da kuma talaucin da ya yi mana katutu.

Sarkin Birnin Gwari, Malam Zubairu Mai Gwari, ya kausasa harshe a kan ’yan siyasar Najeriya wadanda ya bayyana a matsayin mutane marasa kishi da kwadayi ya yi wa zukatansu lullubi.

Basaraken ya yi furucin hakan ne a Kaduna yayin taron tattauna matsalolin da Arewa maso Yammacin Najeriya ke fuskanta wanda wata kungiyar Bincike da Ci gaban Arewa (ARDP) ta shirya.

Sarkin ya bayyana hakan ne a Kaduna yayin taron Arewa maso Yamma kan halin da kasa ke ciki da kuma kalubale a Najeriya wanda kungiyar Arewa Research Development Project (ARDP) da Cibiyar Savannah suka shirya.

A cewarsa, galibin ’yan siyasa a Najeriya na ribatar rashin ilimi da kuma talaucin da ya yi katutu a tsakanin al’umma wajen samun madafan iko.

“Na fadi hakan a lokuta da dama saboda haka ba zai min wahalar maimaita abin da na fada a baya ba.

“Me ya sa ake samun gazawa a cikin ’yan siyasa da ke rike da akalar jagoranci a Jihohi, Kananan Hukumomi da kuma Tarayya?

“Na fahimci cewa wannan matsala tana tattare ne da yanayin ’yan siyasar da muke da su a yankunan mu.

“Duk wani lungu da sako da za ku shiga a kasar nan, wadanda ke kiran kansu ’yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki a sha’anin jagoranci, galibi akwai kwadayi a tattare da su wadanda ke ribatar duk wata dama da suka samu domin su nuna son kansu.

“Wannan shi ne dalili da ba za mu taba cin nasara a al’amuran mu ba saboda a iya sani na duk wanda ke son zama dan majalisar dokoki ko na tarayyya ko Sanata ko Gwamna, yana fitowa ne daga sahun ire-iren wadannan mutane.

“Babu abin da ya dame su da al’ummarsu ko zamantakewa, abin da kawai suka sanya a gaba shi ne tara kudi da dukiya, don haka ta ya za a samu wani kyakkyawan tsari na siyasa a kasar nan?

“’Yan siyasar mu na yanzu abubuwa biyu suke ribata wajen mallakar mutanenmu, abu na farko shi ne rashin ilimi a yayin da galibin mutanenmu suke fama da jahilci saboda haka ake saurin yaudararsu.

“Abu na biyu kuma shi ne talauci, sai kuma na ukunsu shi ne kwadayi da son kai da ya rufewa mutanenmu ido.

“Wadannan abubuwa uku su ne suka hana ruwa gudu wajen inganta tsarin siyasarmu kuma bani da masaniya a kan lokacin da za a samu kyakkyawan jagoranci a kasar nan, saboda mafi akasarin mutanenmu suna fama da rashin ilimi da talauci sannan kuma da kwadayi.

“Mutanen da ke ribatar wannan kasawa ta al’ummar mu su ne ’yan siyasa wadanda suka yi karatu amma kwadayi da son kai ya rufe musu idanu.

“Saboda haka akwai bukatar a yi wa tsarin siyasar Najeriya garambawul,” in ji Mai Gwari.

Ya kuma bayyana kaduwarsa a kan matsalar tsaro da ake fuskanta a kasar, inda ya wassafa wasu daga cikin kalubalen da ake fuskanta musamman a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

A nasa jawaban, Dokta Usman Bugaje, daya daga cikin mahalarta taron wanda aka yi bitar matsalolin tsaro da ake fama da su da suka hada da hare-haren da ake kaddamarwa kan Hausawa a Kudancin Najeriya, ya bayyana cewa wadannan matsaloli da suka dabaibaye kasar na da nasaba da tunkarowar zaben shugaban kasa na 2023 da ke tafe.

A taron wanda jagororin Arewa suka halarta, sun bayyana damuwa kan kisan gillar da ake zargin ’yan awaren Biyafara da yi wa Hausawa mazauna Kudu maso Gabashin kasar, inda suka ce ba tsoro ba ne ke hana su daukar mataki.