✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kwacen wayar marayu ta kai mutum biyu gaban Kuliya

Kotu ta ba da kowane daya daga cikin wadanda ake zargin a kan Naira dubu dari biyar.

An cafke wasu mutum biyu da ake zargi da yi wa wasu marayu biyu fashin wayar salular da suka gada a wurin mahaifinsu.

Tuni aka gurfanar da wadanda lamarin ya shafa a gaban Kotun Majistare da ke Makurdi, babban birnin Jihar Binuwai, bisa zargin aikata laifuka biyu.

A ranar Juma’a aka gurfanar da wadanda ake zargin, inda ake tuhumarsu da laifin muzguna wa marayun da kuma kwacen wayar salula da suka gada a wajen mahaifinsu.

Dan sanda mai gabatar da kara, Insfeta Godwin Ato, ya fada wa kotun cewa a ranar 2 ga Oktoba marayun wanda dukkansu mata ne, suka shigar da korafin abin da ya faru da su a ofishin ’yan sanda na shiyyar ‘B’ da ke Makurdi.

Marayun sun shaida wa ‘yan sanda cewa har duka wadanda ake zargin suka yi musu da barazanar za su kona musu gida, sannan suka kwace wayar da mahaifinsu ya mutu ya bari wadda darajarta ta kai N96,000.

A cewar jami’in, laifukan da suka aikata sun saba wa sassa na 97 da 353 da 398 da kuma 299 na Kundin Dokokin Jihar Binuwai na 2004.

Alkalin kotun, Misis Roseline Iyorshe, ta ba da belin wadanda ake zargin kan kudi N500,000 a kan kowannensu, sannan ta dage shari’ar zuwa ran 14 ga Disamba don yanke hukunci.

(NAN)