Wata Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke zamanta a Dogarawa Zariya ta amince da a mika wa sabon Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli sandar sarauta.
Kotun ta yanke hukuncin ne a karar da Iyan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu ya shigar gabanta yana kalubalantar nadin da aka yi wa Sarki Ahmad Bamalli, yake kuma neman kotun ta hana mika masa sandar sarauta.
- Sarkin Zazzau: Kotu ta tabbatar da nadin Bamalli
- Sarkin Zazzau ya kai ziyarar farko ga Sarkin Musulmi
A zaman kotun na ranar Juma’a, 6 ga Nuwamba, 2020, Mai Shari’a Kabir Dabo ya amince a cigaba da bukin nadin tare da mika wa sabon sarkin sandar sarauta, amma kuma za a ciki gaba da shari’ar.
Lauyoyin bangarorin biyu da masu kara wanda Yunus Ustaz Usman SAN ke jagoranta, sai kuma ba garan masu kareya wanda Abdul Ibrahim SAN lauyan wanda ake kara Na Sarkin Zazzau ke jagoranta.
In ba a manta ba masu karar sun garzaya kotu ne suna kalunalantan matakin Gwamnatin Jihar Kaduna kan nadin, inda suka nemi kotun ta yi watsi da shi, a bi tsarin da aka sani tun shekaru aru-aru na zaben sarki a Masarautar Zazzau.
Kotun ta daga ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 18 ga watan Nuwamba.