✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kuskuren da ake yi game da sakin aure (2)

Matakan ladabtarwa kafin aukuwar saki Akwai matakai uku na ladabtarwa da Allah Ya yi bayaninsu a cikin Alkur’ani sura ta 3 aya ta 34 kamar…

Matakan ladabtarwa kafin aukuwar saki

Akwai matakai uku na ladabtarwa da Allah Ya yi bayaninsu a cikin Alkur’ani sura ta 3 aya ta 34 kamar haka;

1. Wa’azi: Ko shakka babu nasiha na karyar da zukatan mata su fahimci abin da suke yi bai dace ba shi ya sa Allah Ya yi umarni da mu fara yi masu wa’azi a kan hakkokin da suka rataya a wuyansu na daga auren da na mazansu.

2. Kauracewa a shimfida: Amma a nan ba ana nufin namiji ya fice daga cikin gidan ba.  Shi ya sa  Annabi (SAW)ya ce “Kada ku kaurace sai a cikin gida,” kuma ko a cikin gidan ku kasance a daki guda.

3. Bugu/Duka: Amma duka a nan ba na kato da kato ba. Shi ya sa  Annabi (SAW) ya ce “Duka wanda ba mai cutarwa ba.”

Matakan da ake bi don yin saki a Sunnah

Idan kuma duk haka ba ta samu ba, to ga matakan da ake bi idan har za a yi saki, kamar yadda ya zo a cikin Suratul Dalaki:

1 -Kada ka saki mace har sai idan tana cikin tsarkin da ba ka tara da ita a cikinsa ba.

2 -A samu shaidu  biyu adalai.

3 -Mace ta yi idda a dakinta, sai fa idan ta zo da wata alfasha.

A takaice, an shar’anta saki ne a matsayin mataki na karshe na warware turka-turka a tsakanin ma’aurata.

Amma in har akwai wata hanyar mafita kamar yadda ya gabata amma saboda son zuciya ko wata biyan bukata to muna iya kallon wannan mataki a shari’a ya zama haram ko makaruhi a bisa wasu ra’ayoyin malamai.

Insha Allah a darasi na gaba za mu ji ko ya halatta mahaifa ko wadansu makusanta su sakar wa miji matarsa kamar yadda na ji ya auku har kuma matar ta gama idda ta auri wani?

Mafita sai mun tuntubi malamai da masana don kauce wa aikin da-na-sani.

Sanusi Hashim Abban Sultana daga Jihar Katsina.

imel:[email protected]

08065507271