✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

… Kuskure ne a sanya siyasa a ilimin jami’o’in Najeriya – Farfesa Dadari

Wani malami a Sashin Binciken Aikin Gona na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Farfesa Salihu Adamu…

Wani malami a Sashin Binciken Aikin Gona na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Farfesa Salihu Adamu Dadari ya ce bai kamata a rika gina jami’o’i barkatai a Najeriya ba. 

Farfesa Salihu Dadari ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a Jos, inda ya ce ilimi ya tabarbare a Najeriya ne saboda ana sanya siyasa a cikin harkokin ilimin. “Yanzu a Najeriya za ka ga kowane dan siyasa idan ya samu dama, sai  ya je ya dauko jami’a ya kai kauyensu. Ta dalilin haka ne gwamnonin Najeriya suke ta zuwa suna gina jami’o’in jihohi a kauyukansu,” inji shi. 

Farfesa Dadari ya ce jami’o’in nan  9 da aka kafa a zamanin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, idan ka je babu komai a kasa sai gine-gine kawai. Ya ce saboda irin wadannan jami’o’i da ake ta budewa, yanzu jami’o’i sun yi yawa a Najeriya. Ya ce “Bai kamata a rika sanya siyasa a cikin harkokin ilimi ba. Domin ilimi abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar al’umma. Wannan abu da ke faruwa shi ne ya bai wa makarantu masu zaman kansu dama. Duk da cewa makarantu masu zaman kansu ba su kai darajar makarantun gwamnati ba. Amma saboda su ’yan kasuwa ne sukan saya wa yara jarrabawa saboda idan yara suna cin jarrabawa kowa zai kawo dansa, wannan kuma shirme ne.” 

Ya ce ya kamata  gwamnati ta sake lale ta yi amfani da kudin da ake gina sababbin jami’o’in wajen gyara tsofaffin jami’o’in da ake da su a kasar nan, ta hanyar yin gine-gine da samar musu da kayan aiki na zamani. Ya ce yin haka zai ba su damar kara daukar dalibai.

Farfesa Dadari ya ce shirin ciyar da daliban makarantun firamare da gwamnati ta kirkiro ba ya da wani amfani. Ya ce yanzu za ka ga yaran makarantun firamare suna karatu a gindin itatuwa saboda rashin ajujuwa da kujeru. Don haka ya ce gyara makarantun firamare ya fi mahimmanci maimakon bai wa yara abinci.  

Daga nan sai ya yi kira ga iyayen yara su rika kai ’ya’yansu makarantun gwamnati, maimakon makarantu masu zaman kansu, wadanda ya ce suna karatun zuku.