✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kusan mutum 300 sun rasu a girgizar kasa a Afghanistan

Ana fargaban adadin mutanen da suka samu raunuka a iftila’in ya haura 600

Akalla mutum 280 sun rasu, wasu kimanin 600 sun samu raunuka a dare guda a sakamakon wata mummunar girgizar kasa a kasar Afghanistan.

Hukumomin kasar sun ce adadin mutanen da suka rasu da wadanda suka samu raunuka na iya karuwa, a sakamakon wannan girgizar da ta auku kafin wayewar garin ranar Laraba.

Kakakin gwamnatin Afghanistan, Bilal Karimci, ya ce, “An samu girgizar kasa mai karfi, wadda ta yi ajalin daruruwan mutane, ta jikkata wasu daruruwa, tare da rusa gidaje da dama a wasu yankuna hudu da ke Lardin Paktika.

“Muna kira da babbar murya ga hukumomin agaji da jinkai su tura jami’ansu nan take zuwa wuraren, domin takaita tsanantar bala’in.”

Yadda girgizar kasa ta yi barna a Lardin Paktika na kasa Afghanistan
Yadda girgizar kasa ta yi barna a Lardin Paktika na kasa Afghanistan. (Hoto: @alham24992159)

Hotunan girgizar kasar a Gabashin Lardin Paktika ya nuna yadda gidajen kasa suka ruguje, a yayin da masu aikin ceto ke jinyar mutanen da suka jikkata.

Jirage masu saukar ungulu na daukar marasa lafiya kuma sai zirga-zirga suke ta yi suna kwashe mutanen da abin ya shafa daga kauyukan yankin zuwa asibiti.

Girgizar kasar ta auku ne da misalin karfe 1:00 na daren Talata, wato karfe 9 na daren agogon GMT, a yankin da ke da tazarar kilomita 44 daga birnin Khost da ke Kudu maso Gabashin kasar Afghanistan.

Kusan duk shekara a kan samun girgizar kasa a Afghanistan, inda Hukumar Agaji ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana asarar rayuka 560 a duk shekara a dalilin girgizar kasa.

Alkaluman hukumar sun nuna a cikin shekara 10 da suka gabata, Afghanistan ta yi asarar rayuka akalla 7,000 a sakamakon iftila’in girgizar kasa.