Aƙalla mata da ƙananan yara 58 ’yan Najeriya aka ceto daga hannun masu safarar mutane a Ghana.
Wannan ya kawo adadin ’yan Najeriya da aka ceto a Accra cikin watanni uku da suka gabata zuwa 105.
- Ambaliyar ruwa ta lalata ƙananan hukumomi 3 a Kano — SEMA
- Yadda mai tallan kifi ya sayar da zinaren sata N60m a Abuja
Shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyar ’yan Najeriya a ƙetare (NIDO) a Ghana, Cif Callistus Elozieuwa, ya bayyana hakan ga Shugaban Hukumar ’Yan Najeriya a Ƙetare (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa, lokacin da ta ziyarci waɗanda aka ceto a Accra.
Shugaban Sashen Hulɗa da Jama’a na hukumar, Abdur-Rahman Balogun, ya bayyana cewa an ceto mutum 47 ’yan Kano, Katsina (5), Jigawa (2), da Kaduna (4).
Ya ƙara da cewa an kama wasu daga cikin waɗanda ake zargi da safarar mutane kuma an miƙa su ga hukumomin tsaro da Hukumar Hana Safarar Mutane (NAPTIP) don ci gaba da bincike.
Dabiri-Erewa ta yaba wa NIDO Ghana, Jakadan Najeriya na riƙon kwarya a Ghana, da kuma hukumomin tsaro na Ghana kan goyon bayan da suka bayar.
Mata da yaran da aka ceto na kan hanyarsu ta dawowa Najeriya, inda za su samu taimako daga NAPTIP, kafin sake haɗa su da iyalansu.