Kimanin mutane 2,000 sun rasa gidajensu sakamakon ambaliya a al’ummomi daban-daban na kananan hukumomin Gada da Dange-Shuni da ke Jihar Sakkwato.
Daraktan Bada Agaji a Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Sakkwato (SEMA), Mustapha Umar, ya bayyana cewa ambaliyar ta shanye gidaje da gonaki da dama a yankunan.
Ya kara da cewa kimanin mutane 1,700 ne abun ibtilia’in ya shafa a Karamar Hukumar Gada, inda abin ya shanye kimanin hekta 600 na filayen noma baya ga asarar dabbobi da kayan abinci masu yawan gakse.
Ya lissafa yankunan da abin ya shafa a Karamar Hukumar Gada da suka hada da Dantudu da Balakozo da Gidan Tudu da kuam Tsitse.
- EFCC ta gaza gabatar da hujja a kan Kwankwaso a kotu
- ’Yan ta’adda sun fara amfani da jirgi mara matuki —ONSA
- Sheikh Tijjani Guruntum ya gwangwaje dalibansa da kyautar kuɗi da kayan abinci
Sai dai ya bayyana cewa hukumar na ci gaba da bincike kan ibtila’in na Dange-Shuni domin tantance adadin mutanen da abin ya shafa da kuma girman barnar a kararamar hukumar.
A daidai lokacin, jigo a Jam’iyyar APC kuma dan Majalisar Mattijai daga Sokkwato ta Arewa, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya jajanta wa wadanda abun ya shafa.
A sanarwa da kakakinsa, Bashar Abubakar, ya fitar, Sanata Wammako, ya yi musu addu’a tare da rokon Allah kawo musu dauki.