Fira-Ministan Birtaniya Boris Johnson ya tsallake rijiya da baya a kuri’ar yanke kaunar da aka kada kan shi, wacce ba ta yi nasara ba.
Duk da rashin gamsuwar da ‘yan jam’iyyar Conservative mai mulki suke nuna wa da mulkinsa, hakan bai hana Johnson lashe zaben da kuri’a 211 bisa 148 ba.
- Elon Musk ya yi barazanar fasa sayen Twitter
- Musulmai na ci gaba da Allah-wadai da Indiya kan batanci ga Annabi
Nasarar da Johnson din ya samu na nufin nan da shekara guda babu wani kalubale da zai sake fuskanta game da shugabancinsa,
Sai dai kuma, ‘yan adawa 148 daga cikin ‘yan majalisu 359 da tam’iyyar Conservative ke da su, sun kalubalanci mulkin Firaministan.
Boris Johnson ya ce nasarar da ya samu za ta ba shi damar ci gaba da yi wa kasar aiki yadda ya kamata.
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan da bayyana sakamakon zaben, Firaministan ya ce, “Wannan sakamako ne mai kyau, kuma abin da hakan ke nufi shi ne, a matsayinmu na gwamnati za mu ci gaba da ayyukan da jama’a ke bukata.”
An kada kuri’ar jin ra’ayin ce a ranar Litinin bayan da dan jam’iyyar, Graham Brady ya ce ya samu wasiku akalla 54 daga ‘yan jam’iyya inda suka bukaci a kada kuri’ar yanke kauna a Johnson.
Wani tsohon jami’i a gwamnatin Johnson, Leon Emirali, ya bayyana nasarar da Johnsin din ya samu a matsayin ‘sha da kyar’.
Kuma ya ce tsugune ba ta kare mishi ba, sabo a cewarsa akwai babbar matsala da zai fuskanta a gaba.
Gwamnatin Johnson ta fuskanci matsanancin tsaro bayan da wani rahoton bincike ya caccaki gwamnatin da mulkin-kama-karya a karshen watan da ya gabata.