Kamar yadda na yi bayanin kuskuren da mata suke yi wajen zabar miji, sai na ga ya dace in yi adalci, wato in yi magana a kan kura-kuren da maza suke yi wajen zabar matar aure.
Yadda mata suke tafka kuskure a wannan fanni, haka ma maza suke yi wajen zabar matar aure, sai dai za a iya samun dan bambanci tsakanin maza da mata, bisa la’akari da cewa maza su ne suke neman auren mata, ba mata ne ke neman auren maza ba a al’adance.
karya: Tana daga cikin kuskuren da namiji ke yi wajen zabar matar aure. Mafi yawan maza sukan yi wa yarinyar da za su aura karya. Ya rika nuna mata shi mai arziki ko kuma ya fito daga gidan arziki. Wadansu mazan sukan aro kayan sawa da motar hawa don kawai su burge iyaye ko kuma yarinyar da suke neman auren ta. Akwai wadanda suke takurawa kansu su rika kashewa yarinyar da iyayenta kudi, ta hanyar yi musu kyaututtuka masu kayatarwa da ban mamaki.
Wadansu mazan har karyar mukami da sarauta suke yi. Su rika nuna wa yarinyar cewa su ’yan sarauta ne ko kuma mahaifinsa gwamna ne ko minista ko wani mai rike da mukamin siyasa ko kuma wani hamshakin dan kasuwa.
Abin da zai ba ka mamaki shi ne, wasu mazan saboda tsabar karya, sai su saya wa budurwarsu kayan da ba za su taba sayawa iyayensu ko ’yan uwansu na jini ba, don kawai su samu karbuwa a wurin budurwarsu da kuma iyayenta. Wasu mazan sukan yi karyar aiki, su rika cewa suna aiki a wani hamshakin kamfani ko wata babbar ma’aikata, alhali karamar sana’a suke yi.
karanta da Mako: Akwai mazan da tsabar mako ba su iya yi wa budurwarsu kyauta ba. Da zarar wani abu da za a kashe kudi ya taso sai ka ga sun tayar da hankali suna daure fuska, suna fakewa da cewa bai kamata ta rika son su saboda abin duniya ba, kuma suna yin haka ne, saboda kawai tsabar mako. Irin su duk lokacin da za su buga mata waya, ko kunya ba su ji sai su rika yi mata filashin. Mafiyawan mata suna da son abin duniya kuma suna son kyauta.
Gabunta da kauyanci: Wadannan munanan dabi’u ne da mata ba su son su. Idan saurayi ya fiya yawan katobara har mace ta gane shi. To babu shakka za ta tsane shi, amma su mazan da suke da irin wadannan dabi’u, ba su ankara kuma ba su lura da yadda abubuwa suke gudana. Da ya zo hira wurinta ko kuma idan suna magana ta waya sai ya rika yi mata wawanci, saboda rashin iya magana mai dadi da jan hankali.
Mafi akasarin mata sukan so da namiji saboda kalamansa da yadda yake faranta musu rai ta hanyar maganganunsa.
Jahilci: Shi ma yana janyowa mace ta guji namaji. Jahilci babbar cuta ce ga da namiji. Ilimi yana daya daga cikin muhimman abubuwan da ake auna nagartar namiji. Idan ba shi da ilimi ya samu tawaya ta kowane bangare. Wasu mazan ba su gane muhimmancin haka ba, sai ka ga mutum bai kammala karatun sakandire ba, amma yana neman wacce ta kammala digiri.
Wasu jahilan mazan har cewa suke yi ai idan kana da kudi, mace komai iliminta za ka aure ta, kuma ta zauna da kai lafiya, saboda kudinka. To amma sun manta hakan kuskure ne, ko da mace mai ilimi ta auri jahili mai kudi, to babu yadda za su yi daidai, sai raini ya shiga tsakaninta da shi. Mata na son mijinsu ya fi su ilimi, musamman ma na addini, yadda idan ta samu wata matsala za ta tambaye shi ya warware mata.
kazanta: Babu shakka duk namijin da yake kazami ne, ba zai samu karbuwa a wurin mata ba. Wasu mazan za ka ga ba su da tsafta. Kai hatta wanke ba ki wasu mazan ba su yi sai su tafi hira wurin budurwa baki na doyi. Mace na son ta ga namiji cikin tsafta, ta yadda za ta yi alfahari da shi a ko’ina.
Akwai matsalar shisshigi da wasu mazan suke yi wa matan da za su aura da yada jita-jita a kan budurwar da suke nema da gulamce-gulmace da gutsuri-tsoma da tsurku da tsugudidi da cin amana da rashin gaskiya da raini da kuma kananan maganganu. Duk wadannan suna daga cikin kurakuren da maza suke yi wajen zabar matar aure. Allah Ya sa mu dace amin.
Za a iya tuntubar Abubakar ta 08027406827 ko kuma [email protected] ko [email protected]
Kura-kuren da maza ke yi wajen zabar matar aure
Kamar yadda na yi bayanin kuskuren da mata suke yi wajen zabar miji, sai na ga ya dace in yi adalci, wato in yi magana…