A halin yanzu dai kungiyoyin kwallon kafa da dama a nahiyyar Turai sun raba gari da masu horas da ’yan wasansu a kakar wasanni ta bana.
Kawo yanzu dai akwai kimanin kungiyoyin kwallon kafa 15 da suka raba gari da koca-kocansu sakamakon wasu dalilai mabanbanta juna, yayin da kuma wasu masu horaswa ke cikin tsaka mai wuya.
- Sarauniyar Kyau: Har yanzu ji nake kamar a mafarki —Shatu Garko
- Gobara ta kone kamfanin sayar da kayan gado a Kano
Galibi dai rashin katabus da masu horaswar ke yi a kungiyoyin da kuma matsalar matsin tattalin arziki da kungiyoyin ke fuskanta na daga cikin manyan dalilan da ke sa wa ana hannun riga tsakanin kungiyoyin da masu horaswar.
Daga cikin koca-kocan da aka yi waje-rod da su a bayan nan sun hada da na kungiyar Barcelona da Manchester United.
A gasar Serie A kadai, an sallami masu horaswa biyar, sai kuma gasar La Liga inda aka sallami kociyoyi guda uku yayin da a gasar Firimiyar Ingila inda aka sallami kociya shida sai kuma gasar Bundesliga inda kociya daya tal ya rasa aikinsa.
Idan muka soma duba zuwa Kasar Jamus, Mark van Bommel shi ne kociya daya tilo da ya raba gari da kungiyar Wolfsburg a ranar 24 ga watan Oktoba.
Sai kuma a gasar Serie A ta kasar Italiya inda kungiyar Roma ta soma sallamar Paulo Fonseca yayin da ita ma kungiyar Genoa ta raba gari da Davide Ballardini. Sai kuma Fabrizio Castori wanda ya ajiye aikin horaswa a kungiyar Salernitana.
Ita ma dai kungiyar Cagliari ta sallami Leonardo Semplici, sai kuma na karshensu wato Ivan Juric wanda ya ajiye aikin horaswa a kungiyar Hellas Verona.
A gasar La Liga kuma Levante ce ta soma sallamar Paco Lopez, sai Getafe wadda ta sallami José Miguel González Martín da aka fi sani da Michel yayin da Barcelona ta raba gari da Ronald Koeman.
A Firimiyar Ingila kuma, Watford ce soma sallamar mai horaswarta Xisco Munoz, sai Aston Villa wadda ta raba gari da Dean Smith, yayin da Tottenham ta sallami Nuno Espirito Santo, sai dan taki kadan kuma Norwich ta sallami Daniel Parker inda a baya bayan nan da Manchester United ta raba gari da Ole Gunner Solskjær.
Duk dai wadannan kungiyoyi sun raba gari ne da masu horaswar a dalilin rashin tabuka abun kwarai.
Masu sharhi kan harkokin wasanni na ganin cewa wannan lamari na wasu kungiyoyin na raba gari ba ya rasa nasaba da rashin kokari daga bangaren masu horaswa da kuma ’yan wasan kungiyar saboda rashin katabus.
Wasu kuma na ganin cewa rashin hakuri daga bangaren masu kungiyar na daga cikin dalilan da ke sa wa ba a yi wa masu horaswar uzuri duba da irin kudin da masu kungiyar suka zuba wajen cefanen ’yan wasan masu tsada kuma suke hankoron samun riba yanzu-yanzu.
Sai dai kuma ana zargin cewa wasu masu horaswa na fada wa cikin matsala musamman idan ’yan kwallon kafar kungiyar suka juya musu baya.