Gamayyar kungiyoyin kwadago a Najeriya na NLC da TUC sun sanar da janye yajin aikin da suka fara ranar Talata.
Kungiyoyin dau sun tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani ne ranar Talatar domin nuna bacin ransu da dukan da aka yi wa Shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero a Jihar Imo a kwanakin baya.
- Mawaki ya maka BBC Hausa a kotu, yana menan diyyar miliyan 120
- An sace wayar tsohon Minista a cikin kotun Abuja
A lokacin dai Ajaero ya jagoranci ma’aikatan Imo domin wata zanga-zangar nuna rashin jin dadi kan wasu manufofin Gwamnan Jihar, Hope Uzodinma.
Sai dai daga bisani wasu ’yan daba da ake zargin magoya bayan Gwamnan ne suka lakada masa duka sannan ’yan sanda suka tsare shi.
Hakan dai ya janyo fushin kungiyoyin kwadagon, wadanda suka tsunduma yajin aiki a ranar Talata don nuna goyon bayansu gare shi.
Aminiya ya rawaito cewa Mashawarcin Shugaban Kasa kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya sa labule da kungiyoyin a ranar Laraba, a kan yajin aikin, inda ya ce tuni ma aka kama mutum biyu da ake zargi da duka Ajaeron.
Wakilinmu ya jiyo daga wasu jiga-jigan ’yan kwadago yayin taronsu na musamman suna cewa sun amince da daukar matakin ne bayan nazarin dukkan alkawuran da Ribadun ya yi musu.
Shi ma Sakataren kungiyar ma’aikatan gwamnati ta AUPCTRE), Kwamared Sikiru Waheed, shi ma ya tabbatar da labarin ga ’yan jarida.