✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyoyin Ittihadu da WISCOD sun kaddamar da shirin renon yara

kungiyar malaman makarantun islamiyya ta Jihar Filato [Ittihadu Anwaril Hidayat] da kungiyar tallafa wa mata da matasa (WISCOD) sun hada hannu wajen kaddamar da wani…

 Alhaji Yusuf Yahaya, shugaban kungiyar Ittihadukungiyar malaman makarantun islamiyya ta Jihar Filato [Ittihadu Anwaril Hidayat] da kungiyar tallafa wa mata da matasa (WISCOD) sun hada hannu wajen kaddamar da wani shiri na koya wa daliban makarantun islamiyya tarbiyya kan zaman lafiya a garin Jos, babban birnin jihar.
Da yake jawabi a wajen taron kaddamarwa, shugaban kungiyar Ittihadu, Alhaji Yusuf Yahaya ya bayyana cewa an kaddamar da shirin ne don fadakar da dalibansu  kan zaman lafiya a garin Jos, inda suka zabo dalibai 100 daga makarantunsu  17 da ’yan agajinsu 20 don gudanar da shirin.
Ya ce za a rika gabatar da shirin sau daya a kowace ranar Lahadi, har zuwa shekaru uku, ta yadda za  a rika koya wa yaran yanayin tarbiyya da yadda mu’amalarsu  za ta rika kasancewa a gida da makaranta.
Ya ce rashin zaman lafiya da rashin tarbiya ya shafi kowa, don haka dole ne a tashi  a koya wa yara yadda za a zauna lafiya.
Ita ma a nata jawabin, shugabar kungiyar WISCOD, Hajiya Amina Ahmad ta bayyana cewa shirin zai gudana ne  a kan tarbiyyar Musulunci, wadda aka saba koyar da ita a tsakanin musulmi, saboda haka ta yi kira ga  iyaye da malamai da yaran su ba da goyan baya da hadin kai kan wannan aiki, domin a amfana da shi.
A nasa jawabin, shugaban kungiyar iyayen daliban makarantun Ittihadu, Alhaji Ibrahim Sa’ad ya yi nuni ne cewa tarbiyya al’amari ne mai matukar mahimmanci, shi ya sa kungiyarsu ta dade tana gwagwarmaya kan koyar da ita.
Ya mika godiyarsu ga kungiyar WISCOD kan yadda ta kawo wannan shiri a cikin garin Jos.