✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kungiyoyin Ingila sun janye aniyar shiga gasar Super League

Za mu sake fasalin gasar domin ganin hakarmu ta cimma ruwa.

Dukkanin kungiyoyi 6 masu buga gasar Firimiya Ingila, sun janye aniyarsu ta shiga sabuwar gasar Super League ta Turai.

Manchester City ce ta fara ficewa bayan Chelsea ta nuna alamar janyewa daga cikin wannan gasa wacce ta kawo rudani a duniyar kwallon kafa.

Sauron kungiyoyin na Ingilia da suka janye aniyarsu bayan Manchester City da Chelse sun hada da Arsenal, Liverpool, Manchester United da Tottenham.

Haka kuma, Atletico Madrid a Spain da Juventus baya ga Inter Milan da AC Milan daga Italiya, sun fitar da sanarwar janyewa daga gasar.

Sai dai kawo yanzu manyan kungiyoyin Spain biyu da wato Real Madrid da Barcelona ba su ce komai kan matakinsu na goyon bayan gasar ta ESL ba.

Kafofin watsa labaran wasanni sun ruwaito shugaban kungiyar Juventus Andrea Agnelli na cewa, tun bayan ficewar kungiyoyin firimiya 6 ya samu yakinin cewa sabuwar gasar ta ESL ba za ta kai labari ba.

Hakan na zuwa ne bayan da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA), ta yi gargadin cewa kungiyoyin da suka shiga gasar za su fuskanci hukunci, yayin da ita ma Hukumar Kwallon Kafa ta Turai (UEFA), ta ce za ta haramta musu buga gasar cin Kofin Zakarun Turai ta Champions League.

Sai dai mahukunta gasar ta Super League sun ce za su yi nazari kan hanya mafi dacewa wajen sake fasalin gasar domin ganin hakarsu ta cimma ruwa.

Tun da fari dai UEFA ta nuna adawarta da sabuwar gasar, lamarin da ta ce duk dan wasan da ya shiga gasar ba zai buga gasar cin Kofin Duniya ba.

UEFA ta yi Allah wadai da shirin kafa sabuwar gasar da wasu manyan kungiyoyin kwallon kafa a Turai da ake kira European Super League.

Shugaban UEFA, Aleksander Ceferin, ya yi gargadin cewa za a haramta wa duk dan wasan da ya buga gasar wakiltar kasarsa.

’Yan siyasar Turai ciki har da Firaministan Birtaniya Boris Johnson da Shugaba Emmanuel Macron na Faransa, sun yi Allah wadai da sabuwar gasar.

Kazalika, FIFA ta ce ba za ta amince da wannan sabuwar gasa ba, kuma duk wanda ya shiga cikinta, to za ta haramta masa buga gasar cin kofin duniya.

Sai dai wadanda suka shirya sabuwar gasar sun ce za su dauki matakin shari’a domin tabbatar da kafa gasar.

Wata kotu a birnin Madrid na Spain ta gargadi FIFA da UEFA dangane da yunkurin haifar da tarnaki ga wannan sabuwar gasa wadda ta rarraba kawunan masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa a Turai.

Hukumomin kwallon kafa na Turai na ganin cewa, sabuwar gasar za ta yi illa ga Gasar Cin Kofin Zakarun Turai, yayin da ma’assasan sabuwar gasar ke cewa, za ta kawo kudaden shiga fiye da ta cin Kofin Zakarun Turan.