Gamayyar Kungiyoyin Arewa (CNG) sun yi barazanar fara zanga-zanga game tabarbarewar tsaro a fadin yankin.
Kungiyar ta ce muddin gwamnati da kungiyar kwadago ba su mayar da farashin man fetur da wutar lantarki yadda yake a baya ba to babu makawa za ta taro dubban ‘yan zankin su yi zanga-zanga.
Kakakin CNG, Abdul-Azeez Suleiman ya ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba cewa zanga-zangar za ta nuna bacin rai kan tabarbarewar tsaro a yankin ta da kuma ci gaba da rufe jami’o’i da sauran matsaloli.
“Mun fahimci cewa hukumomi sun dage sai sun tabbatar da karin farashin lantarki da man fetur wanda zai fi shafar Arewa fiye da sauran yankunan kasar.
“Ba mu amince da daidaito kan karin farashin da aka cimma tsakanin gwamnati da kungiyar kwadago ba kuma muna kira da a soke shi nan take ba tare da wani sharadi ba”, inji shi.
Karin bayani na tafe….