✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kungiyoyin Arewa sun janye zanga-zanga saboda rikici

Gamayyar Kungiyoyin Mutan Arewa ta nesanta kanta da barnar da aka yi a Edo

Gamayyar Kungiyoyin Mutan Arewa (CNG) ta janye zanga-zangar da suke gudanarwar na kin jinin matsalar tsaro a yankin nan take.

Sanarwar da ta fitar ta nesanta kanta da fasa wurare da ake yi da ma hari da wasu masu zanga-zangar #EndSARS suka kai a Jihar Edo har suka saki fursunoni.

CNG ta ce ba za ta jibanci duk wani nau’i na karya doka ko tashin hankali da sunan zanga-zangar lumanar neman a magance matsalar tsaro a yankin ba.

Don haka ta umarci dukkannin ‘ya’yanta a fadin Arewacin Najeriya da su dakatar da zanga-zangar nan take.

Kakakin CNG Abdul-AAzeez Suleiman ya ce kungiyar ta yaba wa dukkannin wanda suka bi doka wajen gudanar da zanga-zangar #EndSecurityNow cikin lumana, sannan tana Allahwadai da irin aika-aikar da aka tafka a garin na Benin.

Ya kara da cewa, ya kamata masu zanga-zangar #EndInsecurityNow da ke jihohi 19 na Arewancin Najeriya su kasance masu bin doka, sannan kada su yarda a yi amfani da su wajen ta da tarzoma ko kuma bata kayan gwamnati.

“Zanga-zangar #EndSecurityNow ba za ta kasance daya daga cikin abubuwan da za su jawo tashin hankali ba, duba da irin yanayin da ake ciki na bukatar kawo karshen matsalar tsaro da ke damun yankin Arewa da ma Najeriya baki da ya ba”, inji shi.

Har wa yau, CNG ta ce, ba ta goyon bayan dukkanin wani rashin da’a ko wani abu da ya sabawa doka da shari’a a yayin gudanar da zanga-zangar.

A saboda haka ta umarci dukkanin rassanta a jihohin Arewa da su dakatar da zanga-zangar daga Litinin 19 ga watan Oktoba har zuwa lokacin da za a sanar da shirinta na gaba.

Mai magana da yawun kungiyar ya kara da cewa za su ci gaba bibiyar abubuwan da ke wakana tare da gabatar da su ga kungiyar gwamnonin arewa, domin jagoranci nagari.