✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Na dawo Saudiyya ne domin neman ilimi —Ronaldo

Kungiyoyin Turai da Amurka sun so dauka ta amma na zabi Al-Nassr —Ronaldo

Fitaccen dan wasan duniya, Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewa ya koma kungiyar Al-Nassr da ke kasar Saudiyya ne domin samun karin ilimi.

Ronaldo dan asalin kasar Portugal, ya ce kungiyoyin kwallon kafa daga nahiyar Turai da Australia da Amurka da ma kasashen Brazil sun yi masa tayin komawa wajensu, amma ya zabi komawa Saudiyya.

A lokacin da Al-Nassr ke gabatar da shi a matsayin dan wasanta a gaban dubban magoya bayanta a ranar Talata, Ronaldo ya ce, “Na san abin da nake so da wanda ba na so, kuma wannan babban kalubale ne a gare ni na zuwa wannan kasa, ba don komai ba sai don na kara samun ilimi.”

Gwarzon dan wasan ya ci gaba da cewa, “Ina son sabon yanayi, kasa don cimma wani buri na daban tare da Al-Nassr, wannan shi ne dalilin da ya sa na rungumi wannan dama.

“Kamar yadda na fada a baya wannan dama ce a gare ni ba wai a harkar kwallon kafa ba, dama ce da zan sauya tunanin matasa masu tasowa.

“Kungiyoyi da dama daga nahiyar Turai da Brazil da Amurka da Australia da ma Portugal sun so dauka ta amma na yi wannan kungiya alkawari.”

Ronaldo, dan shekara 37 a duniya, ya rattaba hannun zama a Al-Nassr na tsawon shekara biyu da rabi bayan raba gari da Manchester United a watan Nuwamban 2022.

%d bloggers like this: