kungiyar ‘yan kasuwar Minna ta rantsar da sabbin shugabanninta, rantsuwar wanda ya gudana a harabar babbar kasuwar ta Minna ranar Asabar din da ta gabata. Da yake bayani, shugaban kwamitin zaben, Malam Zakariya Sa’idu ya ce zaben ya gudana ne a karkashin kulawar ‘yan kwamitin mutane tara da aka kafa, kuma an yi takara a kujeru 22 ne.
A cewarsa mutane uku ne suka nemi matsayin shugabancin kungiyar yayin da Alhaji Yusuf Muhammad Koshe ya samu nasarar lashe zaben kuma an rantsar da su kamar yadda dokar kungiyar ta nuna.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan karban rantsuwar, sabon shugaban, Alhaji Yusuf Mohammed Koshe ya nemi sauran abokan takararsa da su hada kai su yi aiki tare kamar yadda suka yi yarjejejiya tunda farko, “Wannan kungiya ta ‘yan kasuwa ce ba wani ne zai jagorance mu ba sai mu kan mu da kan mu ‘yan kasuwar, dan haka ‘yan takarar da ba su samu nasara ba, da ma su goyon bayansu duk manufar daya ce, ita ce samarwa ‘yan kasuwa walwala da saukaka masu wajen samun hadin kai da gwamnati da ita kanta kasuwar.”
“Sannan a kowane lokaci kofa a bude ta ke ga dukkan dan kasuwa wajen kai kokensa dan ita kungiyar ta yi tsaye wajen samar da walwala da kyautatawa dukkanin ‘yan kasuwa,” a cewarsa.
Da yake bayani, sakataren hadakar kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa reshen jihar Neja, Malam Yahaya Idris ya ce wannan zabe ya halasta kamar yadda doka ta shirya, dan haka ya jawo hankalin sauran ‘yan takara da su hada kai da zababbun shugabannin kungiya wajen ciyar da kungiyar gaba. A matsayinmu na shugabannin a hadakar kungiyar ‘yan kasuwa ta jiha, mun gamsu da wannan zaben na shugabancin ‘yan kasuwan Minna, sai dai muna jawo hankalinsu da duk abinda za su yi su tabbatar sun bi dokokin kungiya sau da kafa. Barista Kabir Bala Ibrahim ne ya rantsar da sabbin shugabannin wanda kuma nan ta ke suka kama aiki.