✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar ’yan kasuwa a Filato ta koka kan cin zarafin ’ya’yanta

kungiyar kananan ’yan kasuwa da ke kasuwar Terminus a Jihar Filato ta yi zargin cewa jami’an tsaro suna “wuce gona da iri’’ wajen aikin da…

kungiyar kananan ’yan kasuwa da ke kasuwar Terminus a Jihar Filato ta yi zargin cewa jami’an tsaro suna “wuce gona da iri’’ wajen aikin da gwamnati ta sanya su, inda suka ce ana cin zarafinsu.
Shugaban kungiyar Mustapha Ibrahim Bako ne ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a kasuwar, ranar Litinin da ta gabata.
A makon jiya ne gwamnatin Jihar Filato ta kafa dokar hana sayar da kayayyaki a gefen titunan da suka ratsa kasuwar Terminus, inda hakan ya haifar da cece-kuce tsakanin al’ummar jihar.
Mustapha Bako ya yi korafin jami’an tsaron da gwamnati ta sa su aiki sukan wuce kima, inda a yanzu ya ce ta kai suna dukan ’yan kasuwar da suka gani dauke da kayan sayarwa.
Ya ce: “Kodayaushe idan an kafa doka ana samun wanda zai kaddamar da ita, ba za ka kawar da barawo sannan ka bar kaya a kasa ka tafi ba, dole za a samu wanda zai tsare maka kayanka, sannan ba zan ce duka ’ya’yanmu suna jin magana ba, dole sai an samu daidaiku wadanda ba za su ji ba, dama idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai. Amma a gaskiyar lamari tsarin da aka bi bai yi mana dadi ba, saboda gwamnatin nan tamu ce, mu muka zabe ta, muka fada wa mutane canji, yanzu idan an ganmu ma har tsokanarmu ake yi, canji, saboda mu muka dage sai da aka zabi wannan gwamnati, wanda  a yanzu ga abin da take mana,” inji shi.
Shugaban ya bukaci gwamnati ta gina kasuwa kamar yadda ta yi alkawari ba wai daukar wannan matakin da ba zai haifar da “da mai ido ba.”
Ya ce: “Mun so ta gina kasuwa tukunna kamar yadda ta yi alkawarin ginawa. Idan har ta gina kasuwa babu dan kasuwar da zai yi korafi domin an gina kasuwa to za a shiga ciki. Jami’an tsaron da aka cika a kasuwa ya sanya jama’a masu sayan kaya suke tsoro, daga sun tunkaro idan suka ga jami’an tsaro sai su koma, suna jin tsoro, kamar ana wani rikici, don haka muna rokon gwamnati ta rage wadannan jami’an tsaron.”
Ya kuma bukaci gwamnati ta zauna da su don a tattauna yadda za a daidaita al’amarin, domin ko’ina a duniya amfani da bindiga ba ya kawo nasara sai dai tattaunawa.
Ya nemi mambobinsu da su kwantar da hankalinsu su bar wa shugabanninsu komai, kada su manta komai a rayuwa jarrabawa ne, a yanzu suna cikin wata jarrabawa, abin da ya kamata su rika yi shi ne addu’a, a yi hakuri za su bi wannan al’amari kamar yadda doka ta tanadar.
Ya ba gwamnati shawarar komai za ta yi ta rika tuntubar wadanda abin ya shafa don ganin tsarinta ya kai ga nasara.
“Kullum gwamnati takan yi abu ba tare da tuntubar wadanda suka dace ba, saboda tana da jami’an tsaro, amma abin da nake so in sanar da ita shi ne, duk wurin da za ta yi aiki, to ta nemi mutanen wurin, idan ta kama ma ta sanya mutanen wurin a cikin kwamiti, to ta yi hakan, domin za a hadu a yi aikin tare, idan ta yi haka babu wani da zai zo ya rika korafi,” inji shi.