✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar SWAN ta Kano ta dakatar da tsohon shugabanta

Kungiyar Marubuta Labaran Wasanni ta Kasa (SWAN) reshen Jihar Kano, ta dakatar da tsohon Mataimakin Shugaban Kungiyar a Arewa maso Yamma Malam Ado Salisu kan…

Kungiyar Marubuta Labaran Wasanni ta Kasa (SWAN) reshen Jihar Kano, ta dakatar da tsohon Mataimakin Shugaban Kungiyar a Arewa maso Yamma Malam Ado Salisu kan zarginsa da aikata wasu laifuffuka da ta ce sun saba wa dokokinta da suka hada da gudanar da aiki ba bisa ka’ida ba da yi wa sauran mambobin kungiyar zagon kasa.

Mataimakin Sakataren Kungiyar  SWAN ta Jihar, Abdulgafar Oladimeji ya ce kungiyar ta bayyana abin da dakataccen mamban nata Ado Salisu ya nuna a matsayin abin da bai dace ba, kuma ba zai haifar wa kungiyar da ma ido ba.

Ado Salisu yana aiki ne da Gidan Talabijin na Abubakar Rimi kafin kungiyar ta dakatar da shi.

A takardar da Kungiyar SWAN ta rubuta ta dakatarwar ta ce “Daukar matakin dakatarwar ta biyo bayan abubuwan da suka shafi rashin iya gudanar da aiki, rashin biyayya, wadanda abubuwa ne da suka saba wa yarjejeniyar da kungiyar ta cimma.”

Takardar ta sanar da Ado Salisu cewa “Kungiyar za ta kafa kwamiti mai mambobi uku wanda zai binciki abubuwan da aka aikata tare da ba ka dammar kare kanka bisa ga zarge-zargen da mambobin kungiyar ta SWAN ke yi maka, hukuncin da wannan kwamiti zai yanke wanda zai yi aikinsa cikin kwana 90 shi zai bayar da damar sanin matsayinka a cikin kungiyar.”

Takardar ta ce “Daga yanzu za ka koma gefe tare da kaurace wa duk wasu ayyukan Kungiyar SWAN ko bayyana kanka a matsayin mambanta. Idan kungiyar ta kama ka da  wani abu makamancin shiga harkokinta to wannan shi ma laifi ne mai zaman kansa wanda kuma zai iya janyo wani hukunci na  daban.”