Shugabannin kungiyar makarantun Islamiyya masu zaman kansu da ke karamar Hukumar Jos a Jihar Filato, sun shirya wa dalibansu taron muhawara, don tallafa musu.
Da yake jawabi a wajen taron, tsohon ministan watsa labarai da sadarwa, Alhaji Ibarahim Dasuki Salihu Nakande, ya bayyana taron da lamari mai kyau da alfanu a tsakanin daliban makarantun.
Ya ce irin kwazon da daliban suka nuna a wajen muhawarar, ya nuna cewa malaman makarantun kungiyar suna kokari wajen koyar da daliban.
Ya yi kira ga gwamnati ta rika tallafa wa makarantu masu zaman kansu domin su rika samun gudanar da makarantunsu yadda ya kamata.
Tun da farko a nasa jawabin, sakataren kungiyar, Malam Munkaila Baba Hussaini ya bayyana cewa makasundin shirya taron shi ne domin su tallafa wa dalibansu.
“Al’ummarmu suna da bukatar irin wadannan abubuwa na gina yara kan yadda za su rika yin magana a cikin jama’a ba tare da jin tsoro ba. Babban burinmu shi ne mu tallafa wa al’ummarmu da suke koma baya a wajen ilmin boko. Ina kira ga iyaye kan su tallafa wajen biyan kudaden makarantun ’ya’yansu, domin mu sami abin da za mu rika biyan malamanmu a kan lokaci”. Inji shi.
kungiyar shugabannin makarantun Islamiyya ta shirya wa dalibanta taron muhawara
Shugabannin kungiyar makarantun Islamiyya masu zaman kansu da ke karamar Hukumar Jos a Jihar Filato, sun shirya wa dalibansu taron muhawara, don tallafa musu.Da yake…