A daidai lokacin da ake ci gaba da ce-ce-kuce kan hotunan da jarumar Kannywood Rahama Sadau ta saki, Kungiyar Masu Shirya Fina-Finai ta Najeriya (MOPPAN), ta sake nanata dakatarwar da ta yi wa jarumar.
A sanawar da Kakakinta MOPPAN, Al’amin Ciroma ya sanya wa hannu, kungiyar ta ce, “Hotunan Rahama Sadau da suka jawo cece-kuce inda har wani ya yi kalaman batanci ga Annabi Muhammad (SAW) abin takaici ne matuka a wajen MOPPAN.
“Idan ba a manta ba, a ranar 26 ga Oktoba, kungiyar ta dakatar da jarumar daga harkokin masana’antar bayan ta karya wasu dokoki da kuma wasu rashin tarbiyya, inda aka nuna wani bidiyo na wani mawaki Classiq yana rike ta.
- ‘Yan Kannywood Sun Yi Tir Da Hotunan Rahama Sadau
- Rahama Sadau Ta Yi Nadamar Batancin Da Hotunanta Suka Jawo
“Shekara biyu da dakatar da ita, Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano, karkashin jagorancin Malam Isma’ila Na’abba Afakallah a ranar 8 ga Janairun 2018 ta yi wa Rahama Sadau afuwa, afuwar da MOPPAN ta ki amincewa da shi a 15 ga Janairun 2020.
“Don haka, MOPPAN na kara nanata matsayinta na farko a kan Rahama Sadau, kuma tana kira ga dukkan kungiyoyin Kannywood da su yi biyayya ga hukuncin.
“Sannan kuma kungiyar tana so duk kungiyoyin Kannywood da Hausawan duniya cewa ba tare da Rahama Sadau”, inji sanarwar.