✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar Polo ta Katsina ta samu tallafin Naira miliyan 5

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Bello Masari yaba wa kungiyar wasan kwallon dawaki,wato Katsina Polo Kulob gudummuwar Naira miliyan biyar domin cigaba da shirye-shirye tare da…

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Bello Masari yaba wa kungiyar wasan kwallon dawaki,wato Katsina Polo Kulob gudummuwar Naira miliyan biyar domin cigaba da shirye-shirye tare da gudanar da wasan polo na wannan shekara ta 2016 wanda ake sa ran farawa a ranar 20 ga wannan wata na Agusta. Kazalika, gwamnatin jihar ta dauki nauyin yi wa filin wasan kwaskwarima musamman ta yin gyara akan katangar da ta zagaye filin da wasu ‘yan gyare-gyaren da filin ke bukata domin kara inganta wannan wasa mai dadadden tarihi a jihar da kuma kasa baki daya.
Shugaban kungiyar na din-din-din wanda kuma shi ne tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna Alhaji Muhammadu Lawal Kaita, ya yi godiya ga gwamnatin a madadin ‘yan kungiyar a wajen taron kungiyar da aka yi a ranar Lahadin da ta gabata a lokacin da aka sanar da wannan gudunmuwa daga bakin mataimakin shugaban kungiyar,wanda kuma shi ne shugaban cibiyar raya al’adu ta jihar Alhaji Salisu Ado Shinkafi Bunun Katsina.
‘Yan kungiyar sun jinjinawa gwamnatin jahar akan wannan kokari duk kuwa da halin matsin tattalin arzikin da ake fuskanta.
Shi dai wannan wasa na Polo ana bude kakar gasar ce daga Katsina,wanda hakan na nuni da cewa sauran kungiyoyin dake gudanar da wannan wasa sun samu damar cigaba da gudanar da gasar wasan a duk inda suke a cikin fadin kasar kamar yadda tsarin hukumar gudanar da wasan NPF ta kasa ya tsara.
A wajen wannan gasa ta bana dai za a fafata ne a tsakanin kungiyoyin dake fadin kasar nan domin cin kofuna 11.
Kofin Najeriya dai shi ne babban kofi a wajen wannan gasa. Daga nan shi sai kofin marigayi Janar Hassan. Akwai kofin shugaban kasa da na gwamna, sai kofin Ibrahim Zakari da kofin Amadu Commassie da kuma kofin tunawa da Sarkin Katsina Muhammadu Dikko wanda shi ne ya kawo wasan polo daga Ingila zuwa kasar nan a 1920. Sai kuma kofin tunawa da sarkin Katsina Sa Usman Nagogo wanda kuma shi ne dan wasan da ya fi samun alamar a tara (+7) a zamaninsa wanda har ya bar duniya sai da aka dauki tsawon lokaci kafin a samu wanda ya kai wannan matsayi. Sauran kofunan da za a fatata  a tsakanin ‘yan wasan sun hada da na Sarkin Katsina Muhammad Kabir Usman da sarkin Katsina na yanzu Alhaji Abdulmumini Kabir Usman tare da na  shugaban kungiyar Alhaji Mahammdu Lawal Kaita. Har ila yau baya ga gwamnatin jiha, daga cikin masu daukar hidimar yin wannan wasa akwai kamfanin  sadarwar MTN da kuma Magnet Farm.
Ana sa ran za a fara wannan gasar kwallon dawakin ta Katsina ne daga ranar 20 zuwa 27 ga wannan wata na Agusta 2016 in Allah ya kaimu.