Kungiyar Yarabawa ta OPC ta kone wani kauyen Fulani inda ta kashe mace mai juna biyu ta kuma kama wani shugaban Fulanin yankin mai shekara 75 wanda kuma makaho ne.
’Yan OPC sun auka wa yankin Kajola na Jihar Oyo ne a ranar Lahadi, makonni kadan bayan lafawar rikicin kabilanci da ya kai ga masu kayan abinci da shanu sun yi yajin kaiwa yankin Kudancin Najeriya.
- An rufe makarantu a Kwara kan takaddamar sanya Hijabi
- ‘Rikicin Boko Haram ya hallaka mutane 35,000, ya raba 2m sa muhallansu a Borno’
Da yake tabbatar da harin, kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar Oyo, CSP Fadeyi Olugbenga ya ce, “’Yan OPC sun kutsa unguwar Kajola da ke Karamar Hukumar Ibarapa ta Arewa a Jihar Oyo.”
“’Yan sanda sun tabbatar cewa an cinna wa gidan Wakilin Fulani wuta an kuma kone wata mata.”
Aminiya ta gano cewa gobarar da ta tashi daga wutar da ’yan OPC din suka cinna a kauyen ne ya yi sanadiyyar matar makahon.
Olugbenga ya ce “An kai harin ne don kama tsohon, bisa zargin hannunsa a hare-haren wa mutane da manoma Yarabawa.”
’Yan OPC zargin makahon dattijon wanda ake kira Wakili Fulani da zama shugaban masu garkuwa da mutane tare da wasu mutum biyu da suka kama a yankin.
Sai dai Shugaban Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah ta Kasa (MACBAN) Alhaji Abubakar Jijji, ya shaida wa Aminiya cewa harin zai kawo koma-baya ga kokarin da ake yi na samar ya zaman lafiya a Jihar.
“Kwanan nan a kasuwar Bode Musa suka bindige mutanenmu da suka je neman halaliyasu. Suna kashe mana mutane a kan abin da bai taka kara ya karya ba.
“Ko a kwana biyun da suka gabata sai da suka kashe mana dattawa biyu suka kuma yi wa wasu mutum biyar raunin bindiga.
“Muna da hotunansu da duk wasu hujjoji da hukuma ke bukata. Amotekun ta kashe mana mutum uku a Agware. Daga sun je su kwace addunan da Fulani, su kuma Fulanin suka ki yarda sai suka hahharbe su.
“Ya kamata su san cewa babu yadda za a yi Bafulatani ya kasance ba tare da wuka ko adda ba saboda da su suke amfani wajen yanka dobbobinsu da suka kasa.”
Kakakin ’yan sandan ya ce, “A halin yanzu mutum na tsare a hannunmu kuma Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Oyo ya sa a kai Wakili asibiti saboda raunin jikinsa, sauran kuma a ci gaba da binciken su.
“Sauran wadanda ake bincikin ’yan OPC ne ake zargi da kisan kai da kuma kone-konen.”
Shugaban Miyetti Allah na Jihar Oyo, ya yi tir da harin wanda ya ce tsantsar zalunci ne ’yan OPC da kungiyar Amotekun ke wa al’ummomin Fulani a Jihar.