Kungiyar Matasan Musulmin Kudancin Kaduna, (MYFOSKA), ta shirya taron bita na yini guda a garin Kafanchan kan muhimmancin hadin kai da mallakar katin zabe da samar da tsaro kafin da kuma kiyaye duk wani abu da ka iya haifar da matsala a lokutan zabubbukan da ke tafe.
Kungiyar, ta bakin shugabanta na kasa Malam Kabir Muhammad Bello, ta yi kira ga Musulmi su sauna lafiya a tsakaninsu da kuma a tsakaninsu da wadanda ba Musulmi ba sannan su guji yaga hotunan ’yan takara ko zafafa muhawara marar amfani tare da kiyaye harshensu.
“Muna kira gare ku da ku tabbatar kun mallaki katin zabe tare da zabar ’yan takarar da suka dace kuma kuke so a bisa zabinku,” inji shi.
Kungiyar ta yi kira ga al’ummar Musulmi su tabbatar sun yi rajistar katin zabe da yi wa ’ya’yansu rajistar katin zama dan kasa da na haihuwa da kuma na rasuwa idan an yi rashi tare da Hukumar Kidayar Jama’a ta Kasa.
A karshe ta yi kira ga jama’a su ci gaba da yin addu’o’in zaman lafiya tare da samuwar shugaba nagari da zai kawo zaman lafiya da ci gaba a Kudancin Kaduna da jihar da kuma kasa baki daya.