✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Muryar Talaka ta shiga rikici

A ranar Juma’ar da ta gabata ce Kungiyar Muryar Talaka ta gudanar da babban taronta a Gusau, Jihar Zamfara, inda taro ya hadu da wasu…

A ranar Juma’ar da ta gabata ce Kungiyar Muryar Talaka ta gudanar da babban taronta a Gusau, Jihar Zamfara, inda taro ya hadu da wasu matsalolin da suka sanya wadansu shugabannin jihohi ficewa daga zauren taron cikin fushi.

An kira taron ne saboda karewar wa’adin zababbun shugabannin kungiyar na kasa, kuma dukanin shugabannin kwamitin zartarwa na jihohi da wakilai da iyayen kungiyar sun halarta. Sai kuma manyan baki da suka hada da mai masaukin baki, Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Malam Muhammad Ibrahim Wakkala da Farfesa Aliyu Jibiya na Jami’ar Bayero da Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Farfesa Abdullahi Shinkafi da sauransu.

A jawabin Shugaban Kungiyar ta Kasa, Alhaji Zaidu Bala Kofa Sabuwa ya yi godiya ga ’ya’yan kungiyar bisa hadin kai da ya samu wanda ya sa ya cimma nasarar da suka samu. Kuma ya jinjina wa iyayen kungiyar wadanda suke ba ta goyon baya a tsawon lokaci.

A jawabin daya daga cikin iyayen kungiyar kuma Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Malam Muhammad Ibrahim Wakkala ya jinjina wa kokarin shugabannin, sannan ya yi kira ga dukan jagororin kungiyar da suka halarci taron su dubi matsayin kungiyar tare da yin karatun ta natsu, kafin su yanke hukunci kan abin da za su gabatar a wurin taron. Ya ce tun farko an tattauna tsakanin shugabannin kungiyar da iyaye da kwamitin amintattu a kan bukatar tattaunawa da mambobin kungiya, sannan duk matsayar da aka cimma ita ce wakilan kungiyar daga jihohi za su gabatar a wurin taron.

Bayan kammala jawabinsa ne aka fara gayyato shugabannin jihohi domin bayyana matsayinsu a kan jagorancin shugabanni na kasa kan a sabunta musu wa’adin ko a rusa su? Jihohi 12 cikin 14 da suka halarci taron sun amince da bukatar shugabannin su ci gaba da rike kungiyar har zuwa lokacin da za a gudanar da zabe na gaba. Amma jihohin Gombe da Jigawa suka nuna kin amincewa, inda hakan ya haifar da korafe-korafe tsakanin ’ya’yan kungiyar.

Daga baya, Zaidu Bala Kofa ya bayyana cewa har yanzu shi ne shugaban kungiyar “An gudanar da taro gaban jama’a ciki har da ’yan jarida, amma wadanda ba a bi ra’ayinsu ba suke ta korafi, kuma hatta masu sanya ido a kan taron su Farfesa Aliyu Jibiya da wakilin Sarkin Katsinan Gusau sun yaba da yadda aka gudanar da zaben cikin adalci, kuma sun bukaci wadanda ba su ji dadin sakamakon ba su rungumi kaddara,” inji shi.

Shugaban Kungiyar ta Jihar Gombe, Kwamared Affan Buba Abuya ya bayyana taron da marar tushe kuma marar inganci. “Muna da tsarin zaben shugabanni daga matakin kasa zuwa jihohi, kuma wa’adin shugabannin na kasa ya kare tun a watan Yunin da ya gabata, amma sun ki sauka. Ba ma shekara hudu ba, tun da aka kafa kungiyar fiye da shekara tara su ne ke jagoranci, kuma babu wanda ya ce don me? Amma yanzu tunda wa’adinsu ya kare muka ce su sauka, kuma ba za mu taba amincewa ba har sai an sake zabe,” inji shi.

Ya kara da cewa: “A zatonmu taron irin wanda aka saba yi ne, wato za a hadu a tsara yadda za a sake sabon zabe a kafa kwamiti da sauransu, amma sai aka sanar da cewa shugabannin za su ci gaba da jagoranci kamar yadda Mai girma Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara ya goyi baya. Ka ga wannan saba ka’ida ce, kuma rashin adalci ne. Ba wai muna kin jinin Zaidu ba ne, a’a, ya zo shiga zabe, idan ya sake ci shi ke nan, amma irin wannan kama-karya ne ba za mu amince da shi ba,” inji Affan.