Kungiyar Miyetti Allah ta kai taimako ga fulanin da rikicin makiyaya da manoma ya shafa a cikin kananan Hukuman Numan da Demsa da Kikon na Jihar Adamawa.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah a yankin Arewacin Najeriya, Umar Mafindi ya ce sun kai wadannan taimakon ne domin ganin irin halin da fulani suka shiga na wahalar rayuwa bayan kona musu gidaje da aka yi sakamakon rikici da ya auko a tsakanin manoma da makiyaya domin samar masu saukin.
Shugaban karamar Hukumar Demsa, Musa Adamu ya ce ya yi matukar farin ciki game da taimakon da aka basu kuma babu abin da zai iya cewa sai dai Allah Ya saka musu da alheri.
A cikin kayayyakin da aka bai wa wadanda rikicin ta shafa akwa buhunan masara da magi da sauransu.