Kungiyar mata ’yan jarida ta kasa reshen Jihar Gombe (NAWOJ) ta bi sahun takwarorinta a fadin Najeriya wajen shirya gangami na musamman don yi wa kasar addu’o’i bisa halin da ta tsinci kanta a ciki na yawan zubar da jini da satar jama’a don neman kudin fansa.
Shugabar kungiyar a Jihar Gombe, Uwargida Comfort Ali Mukollo ce ta jagoranci tawagar kungiyar mata ’yan jaridar wajen gudanar da wanann taro.
- ‘Mun kwato Dala miliyan 153 a hannun tsohuwar Ministar Man Fetur’
- Sheikh Dahiru Bauchi ya gudanar da Idin karamar sallah
Mambobin kungiyar sun yi gangamin ne sanye cikin jajayen kaya don nuna takaicinsu kan yadda ake zubar da jini a kasar tare da gabatar da addu’o’in kawo karshen ayyukan ta’addanci da rashin tsaro da ke addabar tattalin arziki da kuma zamantakewar al’umma a kasar.
Uwargida Comfort Ali Mukollo, ta ce mafita ga wannan yanayi da ake ciki a kasar shi ne kawai mutane su koma ga Allah a dukufa wajen gabatar da addu’o’i don ganin karshen lamarin.
Ta yi kira da a ci gaba da jajircewa wajen yi wa kasar addu’a dan kawo karshen ta’adar masu garkuwa da mutane da sauran kalabalen tsaro da ya dabaibaye kasar
Kazalika, ta ce wannan taron addu’a an gudanar da shi ne a daukacin jihohin Najeriya 36 da birnin Tarayya Abuja, don Mai Duka ya kawo karshen tashe-tashen hankula da ta’addanci da sauran ayyukan bata gari da suka hana ruwa gudu a kasar.
Yayin taron wanda ya hada dukkan mabiya addinai na Musulmi da Kirista, kungiyar ta janyo hankalin sauran masu ruwa da tsaki da su himmatu wajen ba da ta su gudunmuwar a kan kyautata zamantalewa tsakanin dukkan ’yan kasa ba tare da nuna wariyar addini ko jinsi ba.