✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar Masu Kayan Marmari sun zabi sabbin shugabanni

kungiyar Masu Sayar da Kayan Marmari na yankin Babban Birnin Tarayya Abuja sun zabi sabbin shuganni da za su ja ragamar kungiyar na tsawon shekara…

kungiyar Masu Sayar da Kayan Marmari na yankin Babban Birnin Tarayya Abuja sun zabi sabbin shuganni da za su ja ragamar kungiyar na tsawon shekara hudu.
Zaben ya gudana ne a farkon makon da ya gabata sannan a ka yi bikin rantsar da shugabbanin tare da mika masu shaidan nasara a karshen mako da ya gabata wanda ya gudana a babban kasuwar kayan marmari ta Abuja da ke unguwar Zuba.
A jawabin da ya yi a madadin daukacin ’yan kwamitin zartarwa da a ka zaba, sabon shugaban kungiyar Malam Shafi’u M. Yahaya ya bayyana godiyarsa ga mambobin kungiyar a kan zabarsu da su ka yi tare da alwashin kyautata yanayin kasuwar, inda ya bukaci goyon baya don samun nasara. Tshohon Shugaban kungiyar Malam Nura Haruna wanda ya sha kayi a zaben da ya gabata, ya yi alkawarin ba da goyon bayansa ga sabon shugaban da ’yan majalisarsa sannan ya bukace shi da ya rungumi kowa.
Babban bako a wajen bikin wanda shi ne dan majalisar wakilai mai wakiltar Abuja-ta-Kudu Alhaji Zakari Angulu Dobi ya bayyana muhimmancin kasuwar a yankin birnin tarayya da kewaye. Har ila yau, ya kuma yi alkawarin isar da bukatar ’yan kungiyar na inganta kasuwar ga sabon Ministan Abuja Alhaji Muhammad Bello wanda ya bayyana a matsayin haziki a lokacin da ya rike shugabancin hukumar alhazai ta kasa.
Sauran wadanda su ka halarci taron sun hada da Mai Unguwar Zuba Malam kasim Muhammad da ya wakilci Agoran Zuba Alhaji Muhammad Bello, da kuma sauran man’an baki.