A makon jiya ne kungiyar Marubuta ta Najeriya, reshen Jihar Kano, a karkashin shugabancin Malam Zaharaddeen Ibrhaim Kallah ta gudanar da kwarya-kwaryan biki na tsawon mako daya da zimmar bunkasa Adabi a jihar da kasa da ma duniya baki daya.
Bikin wanda aka yi wa take da “Makon Adabi A Kano,” an shirya shi ne kacokan domin motsa hazon harkokin karatu da rubutu a cikin al’umma, al’adar da ta fara yin sanyi musamman tsakanin matasa maza da mata. Kadan daga cikin muhimman harkokin da aka gudanar a makon na jiya, sun hada da tarukan kara wa juna sani ta bangaren karatu da rubutu na kirkira, koya wa matasan marubuta dubarun tallata hajarsu a intanet, karrama muhimman mutane na ciki da wajen Jihar Kano da suke yi wa Adabi hidima da sauransu.
Tsarin bikin ya faro ne tun daga ranar Talatar makon jiya (28-11-2017), inda masana, marubuta na da da na yanzu, malaman addini da malaman jami’a da ’yan jarida daga sassa daban-daban na kasar nan suka halarci bikin. An bude taron ne a Zauren Karatu na Mahmud Tukur da ke a tsohuwar harabar Jami’ar Bayero, Kano a karkashin jagorancin tsohon Shugaban Cibiyar Shirya Jarabawa ta Najeriya (NECO), Farfesa Abdurrashid Garba.
A yayin taron, an baje kolin littattafai, an yi jawabai, manyan mutane sun yi karatu daga wasu zababbun littattafai domin jan hankali ga al’umma, musamman yara da matasa su dauki ta’adar karatu. Haka kuma an gudanar da gasar rubutun kirkirarrun gajerun labarai ga daliban makarantun sakandare na Jihar Kano.
Kadan daga cikin muhimman mutanen da suka yi karance-karance domin jan hankalin yara, sun hada da mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II da shahararren malamin Musulunci, Shaikh Ibrahim Khalil da fitattun marubuta, kamar Ado Ahmad Gidan Dabino da kuma Umar S. Jigirya. A yayin da shi sarki ya gudanar da karatun a fadarsa, gaban yara, sauran malaman sun gudanar da nasu karatun a zauren taron da ke jami’a.
An gudanar da wani gagarumin taron kara wa juna sani, inda aka samu hadin gwiwa tsakanin kungiyar Marubuta ta Najeriya Reshen Jihar Kano da kuma kungiyar Marubuta ta Jami’ar Bayero. Shugaban Tsangayar Nazarin Shirin Fim da Wasannin Kwaikwayo ta Jami’ar Bayero, Farfesa Muhammad O. Bhadmus ne ya shugabanci taron, a yayin da tsohon Darakta-Janar na Hukumar A Daidaita Sahu, Malam Bala Muhammad ne ya kasance mai gabatarwa. Sauran manyan da suka kasance a wurin sun hada da Malam Zaharaddeen Ibrahim Kallah da Tijjani Muhammad Musa da Dokta Gausu Ahmad da Malam Isma’il Bala da Bilkisu Elyakub da Abdulkadir Badsha Mukhatar da A’isha Umar Sanusi da sauransu.
Wani muhimmin al’amari da ya gudana a ranar Larabar makon jiya, shi ne gasar keke-da-keke da aka shirya ga daliban makarantun sakandare na Jihar Kano, wanda aka shirya musamman domin dibiya wa yara dabi’ar karatu da rubutu. An gudanar da gasar bangarori biyu, Ingilishi da Hausa.
A bangaren Hausa, makarantar sakandare ta Gora Academy ce ta lashe gasar, sai GTC Nassarawa ta take mata baya, sai kuma Shekara GGS ta biyo sahu, inda kuma Khalil Arabic Secondary School ta samu matsayi na hudu.
A bangaren Ingilishi kuwa, makarantar Creatibe Minds Academy ce ta lashe, sai Fatima Muhammad GGS ta zo ta biyu, Kano Capital Girls College ta zo ta uku, inda daga karshe Khalil Arabic Secondary School ta zama ta hudu.
A rana ta uku kuwa, wacce ta kasance Alhamis, masana a harkokin kasuwancin zamani ta intanet, sun shirya wa marubuta masu tasowa hikimomin kasuwancin littattatai da sauran ayyukan adabi ta hanyar fasahar intanet. An gudanar da wannan bita a dakin Karatu na Murtala Muhammad Kano, inda masana harkar, Malam Abdulkarim Muhammad da Sulaiman Umar da Muhammad Goni Muhammad suka kasance jagororin shirin.
Wani shiri kuma da aka gabatar, shi ne taron kalubale, inda aka gabatar da wasu tsofaffi da sababbin marubuta ga manazarta da makaranta. An samu musayar ra’ayoyi da shawarwari da tambayoyi da amsoshi daga marubutan da kuma manazarta da makaranta.
Taron wanda marubuci Ado Ahmad Gidan Dabino (MON) ya jagoranta, ya hada da marubuta, Bala Anas Babinlata da Bilkisu Yusuf Ali da Hauwa Lawan Maiturare da Maimuna Idris Sani Beli.
A ranar Jumu’a (1-12-2017) da misalin karfe hudu na yamma ne aka gudanar da gagarumin biki na karshe a makon, wanda ya kasance taron karramawa da mika kyaututtuka ga muhimman mutanen da suka dade suna ba da gudunmowa ta fuskar bunkasa adabi. Haka kuma an mika kyaututtuka ga daliban da suka fafata a kasannin da aka gabatar tsakanin makarantun sakandare na Jihar Kano.
A yayin bikin, wanda Farfesa Adamu Yusuf na Jami’ar Bayero Kano ya shugabanta, an karrama wadannan muhimman mutane, ta hanyar mika masu kambi iri daban-daban: Sarkin Kano Muhammad Sanusi II da Sam Nda-Isaiah da Dokta Wale Okediran da Farfesa Isah Mukhtar da Sanusi Shehu Daneji da Hukumar Kula da dakunan Karatu ta Jihar Kano da dakin Karatu na Amurka da ke harabar dakin Karatu na Murtala Muhammad Kano.
Sauran sun hada da Maigari Ahmad Bichi da Auwalu Yusuf Hamza da Sa’adatu Baba Ahmad da Garba Ibrahim Tsanyawa da Sadiya Garba Yakasai da Kabir Yusuf Anka da Nazir Adam Salihi da Farfesa Faruk Sarkin Fada da Yahaya dan Arewa da Dokta Tijjani Almajir da Bashir Yahuza Malumfashi da Nasir G. ’Yan Awaki da kuma Fauziyya D. Sulaiman.
Tun da farko, kasancewar rana ce da ta dace da murnar haihuwar Manzon Allah (saw), a gaban dinbin mahalarta taron, Bashir Yahuza Malumfashi ya rera wadansu baitocin yabo, wadanda ya sanya wa taken “Sha Yabo: Muhammadu (saw).”
A lokacin jawabinsa, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, wanda ya samu wakilcin dan Malikin Kano, Ambasada Ahmad Umar ya ce “Sarki ya yi matukar farin ciki da yunkurin marubuta na ganin sun farfado da al’adar karatu da rubuta a tsakanin al’ummarmu. Kuma ya sha alwashin ci gaba da ba da tallafi da goyon baya ga marubuta a kowane lokaci.”
Shi kuwa Shugaban kamfanin wallafa jaridun Leadership, Sam Nda-Isaiah, murna ya yi da wannan kyauta sannan ya kara yaba wa daukacin marubutan Jihar Kano. A cewarsa, “A yayin da wasu jihohi ke bugun gaba da albarkatun kasa kamar man fetur da abinci da sauransu, ni kuwa ina ganina babbar albarkar da Kano ta mallaka, ita ce ta dinbin marubuta.”
Mafi yawan mahalarta bikin sun yaba wa Shugaban kungiyar Marubuta ta Najeriya reshen Jihar Kano, Malam Zaharaddeen Ibrahim Kallah, saboda jajircewarsa da kokarinsa wajen shirya wanan babban biki, wanda ya taimaka sosai wajen farfado da martabar marubuta da harkar rubutu tsakanin matasa da kuma jawo hankalin shugabanni da masana da sarakuna game da muhimmancin adabi ga al’umma.