✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar marubuta ta Kano ta zabi sababbin shugabbanni

kungiyar Marubuta ta Najeriya (ANA) reshen Jihar Kano ta gudanar da zaben sababbin shugabanni, wadanda za su rike ragamar shugabanci tare da zartar da al’amuranta…

kungiyar Marubuta ta Najeriya (ANA) reshen Jihar Kano ta gudanar da zaben sababbin shugabanni, wadanda za su rike ragamar shugabanci tare da zartar da al’amuranta zuwa shekaru biyu masu zuwa.
An gudanar da zaben ne a babban dakin taro na tunawa da Murtala Muhammad da ke birnin Kano yayin babban taron shekara-shekara da kungiyar da ta saba gudanarwa.
A wani rubutaccen sako mai dauke da sa hannun sabon jami’in hulda da jama’a na kungiyar, Ahmad Muhammad danyaro, ya ce, an zabi sababbin shugabannin ne wadanda ake sa ran za su kawo sauyin alkibla na al’amuran kungiyar tare da tafiyar da al’amuranta na tsawon shekara biyu.
Sabon shugaban kungiyar, Badamasi Shu’aibu Burji ya sha alwashin daukaka martabar kungiyar.
Ya ce: “A halin yanzu da za mu kama aiki, ina yi wa mambobin kungiya alkawarin daukaka martabar kungiyar marubuta ta Najeriya reshen jihar Kano, zan yi kokarin zakulo masu basira daga cikin matasan marubuta ta yadda za a zaburar da su wajen nuna hazakarsu.”
A karshe ya bukaci ’yan kungiyar su hada kansu don daga darajar kungiyar.
Sababbin shugabannin su ne: Shugaba, Badamasi Shu’aibu Burji; Mataimakin Shugaba, Muhammad Lawal Barista;  Sakatare, Al-Mustapha Sani Iliyasu; Mataimakin Sakatare, Aminu Salisu Giginyu; Ma’aji, Isyaku Umar Maikudi; Sakataren Kudi, Kabiru Yusuf Anka.
Ahmad Muhammad danyaro, shi ne Jami’in hulda da jama’a na bangaren Turanci; Aminu Yusuf Indabo, jami’in hulda da jama’a na bangern Hausa da Sani Abbas Sa’id, jami’in walwalar jama’a da Abba Shehu Musa, mai ba da shawara ta bangaren shari’a da Nasiru ’Yan Awaki, mai binciken kudi na I da Lawan Giginyu, mai binciken kudi na II
Dattawan kungiya sun hada da: Isma’ila Garba da Zahraddeen Ibrahim Kallah da Tijjani Almajir da Yaseer da kuma Ibrahim Kallah.