Gamayyar matan musulmi da kirista karkashin kungiyar ‘Majalisar Mata Musulmi da Kirista (Women’s Interfaith Council) ta Jihar Kaduna ta shirya taron addu’o’i don karfafa gwiwa ga sauran gamayyar kungiyoyin mata musulmi da kirista da ke kudancin Jihar Kaduna a garin Kafanchan da ke karamar Hukumar Jama’a tare da fadakarwa kan muhimmancin zaman lafiya.
A lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron, Kwamishinan al’amuran kananan Hukumomi da masarautu na Jihar Kaduna, Farfesa Kabir Mato ne ya bayyana cin hanci da rashawa da rashin tausayi da ya yi wa shugabanni katutu a kasar nan a matsayin dalilan tashe-tashen hankula da rashin zaman lafiya da kasar nan ta fada ciki.
Farfesa Kabir, ya kuma bayyana rashin iya shugabanci a Najeriya ne ta sa hatta kananan kasashen da ba su kai Najeriya arziki ba suke samun cigaba cikin sauri fiye da Najeriya, inda ya bayyana salon shugabanci a Najeriya a matsayin ummul haba’isin fadawar Najeriya cikin halin ni ‘ya su ta yadda mai uwa a gindin murhu ne kawai ke samun abin da ya ke so. “Sun mayar da arzikin kasa tamkar dukiyarsu ta yadda su ke baiwa wanda suka ga dama su kuma hana wanda su ka ga dama.” Farfesan ya kuma nuna takaicinsa kan yadda malamai su ka maida kan su ‘yan siyasa.
Da ya juya kan mata, farfesan ya yi kira gare su da su a matsayinsu na wadanda su ka fi fadawa cikin wahala da barazana a yayin rikici, da su zamo jagorori wajen bayar da kyakkyawan misali na zaman lafiya.
A lokacin da yake na shi jawabin, shugaban riko na karamar Hukumar Jama’a kuma mai masaukin baki Alhaji Yusuf Usman Mu’azu ya bayyana muhimmancin da mata ke da shi wajen samar da sauyi a cikin al’umma, dalilin da ya sa suka dade suna dakon shirya irin wannan zama, inda ya nuna farin cikinsa ga wannan kungiyar da ta shirya wannan taro sannan ya mika godiyarsa ga gwamnan jihar Kaduna da bias kokarinsa na samar da zaman lafiya a kudancin jihar.
Da ta ke karin haske kan makasudin shirya taron, babbar daraktar kungiyar Rabaran Sista Anne Falola, ta bayyana mata a matsayin kashin bayan samar da zaman lafiya ko akasinsa, ta yadda a wasu lokuta su ke ingiza mazajensu kan daukar fansa ko tayar da fitina, inda tayi kira gare su da su rika cusa tarbiyya nagari da kuma kaunar juna a zukatan kananan yaransu domin su ne tubulin farko na ginin al’umma.
Wakilin Bishop na Katolika na kudancin Kaduna Bishop danlami Bagobiri, Rabaran Andrew Anana da na’ibin limamin masallacin jumma’a na garin Kafanchan Muhammad Kabir kassim (Alhaji Mami) ne su ka wakilci malaman addinin kirista da na musulunci.
Taron, wanda aka gudanar da shi a dakin taro na otel din Wonderland da ke garin Kafanchan ya kunshi wakilan kungiyoyin mata musulmi da kirista ne daga kananan Hukumomi takwas da ke kudancin Kaduna.